Labarin Burgewa kan Michelle Ekure wadda Ta Kammala Makaranta

Labarin Burgewa kan Michelle Ekure wadda Ta Kammala Makaranta

 -Michelle Ekure wadda ta karanci International Studies ta koma yin takalmi abinda ze ba mutane da yawa mamaki.

A wannan lokacin da muke ciki na karuwar rashin aikinyi,wata kyakykyawar yarinya ta fara wani aiki wanda yawanci mutane irinta baza ka same su sunayi ba. A tattaunawar da sukayi da Lukman na Wazobia Global Time USA wanda aka yadda a buga a Lailaa Blog,Michelle ta bayyana yadda akayi har ta zama mai yin takalmi.

Labarin Burgewa kan Michelle Ekure wadda Ta Kammala Makaranta
Labarin Burgewa kan Michelle Ekure wadda Ta Kammala Makaranta

Tace" Na kammala karatuna na jami'a shekara 6 da ta wuce,inda na ta neman aiki amma ban samu ba,a wani lokaci dai na samu wani aiki a wani kamfani a lagos,amma mai gidan mu yana yawan rike mana kudi a matsayin bashi saina dena.  Yadda na fara, akwai wani kamfani aa lagos inda bake sayen takalmi ina saayarwa,suna da takalma masu kyau,na ce a raina wata rana zan fada ma mutanen nan su man takalmin da zan sa, hakan akayi kuma, naje na fada masu suka yarda. Ta haka na samu aka man takalmina na kaina, wani abokina aa gabatar da ni gurin wani da ke yin takalmi, ina kallon yadda ya hada wata rana abin ya ban sha'awa, sai na tambayeshi ko zai koya man sai kuma ya yarda ya koya man.

KU KARANTA : Yan fashi sun kashe wani mai babur

Ta bayyana yadda ta ke sai da takalmi.        "Ina sayarwa kai tsaye,amma na fi samun sayarwa taa hanyar dandalin sadarwa kamar Instagram,Facebook,tweeter. Michelleather tana sayarda kafar takalmi kamar 50 a sati. Taba yan uwanta yan mata shawara kar suyi tayin yawon neman aiki,suyi kokari su kirkiri wani abu na kasuwanci dan cigaban raayuwar su.      "Kullun ina fadama mutanen da nake haduwa da su da suke neman aiki da s fara wani abu da suka san sun iya, ze iya kawo masu abin kashewa ko kuma su koyi sana'a.

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng