Karanta dalilin da yasa maza ke gajiya da matayansu

Karanta dalilin da yasa maza ke gajiya da matayansu

Bisa ga abubuwan da ke faruwa a tsakanin jama’a, an lura cewa mazaje na gajiya da matayensu yan watanni kadan bayan auransu. Zai suji sun gaji da zama da matar da suka yi rantsuwar kasancewa tare da har karshen rayuwarsu jim kadan bayan sunyi aure.

Karanta dalilin da yasa maza ke gajiya da matayansu

Mazaje na jin sun gaji dan lokaci kadan bayan auran yayin da suka fara ganin canji a abubuwa ba kamar yanda suke a da ba. Wannan na ba mutane mamaki kan dalilin da yasa majaze ke gajiya da matayensu dan lokaci kadan bayan auransu.

Yayin da a dayan bangaren, mataye ke jin dadin son nuna wa duniya cewa matsayinsu ya canja daga budurwa zuwa matar aure. Da zaran anyi aure komai yake komawa daidai a bangaren maza. Zasu koma bakin ayyukansu wasu kuma su koma tafiyar da rayuwarsu kamar yanda yake a da.

A wasu lokutan ma, da wuya ka gane idan namiji na da aure saboda yanda yake abubuwa a cikin jama’a yayin da mace take son mutanen dake kewaye da ita su kirata da sabon sunanta na matar aure. Shin mata sun fi daukar aure da muhimmanci ne?

Ga wasu dalilai dake sa maza suji sun gaji da matayensu da zaran anyi aure:

1.Rashin kwalliya da gyaran jiki: wasu matan basa kula da jikin su da zaran sunyi aure domin suna ganin cewa wa zasuyi ma kwalliya tunda sun ridaga sunyi aure.

Karanta dalilin da yasa maza ke gajiya da matayansu

2.Da zaran mace ta fara haihuwa: wasu mazajen basu iya hakuri da mata a lokacin da suka samu ciki, saboda irin ifface-ifface da sukeyi a wannan lokaci kamar irin su amai da sauransu. Yayin da wasu mazan ke fara harin yan matan waje saboda suna ganin ta gida ta tashi aiki ya kamata su nemi sabuwar jinni.

Karanta dalilin da yasa maza ke gajiya da matayansu

3.Rashin fahimatar juna: Yana da kyau sabbabin ma’aurata su kasance tare a ko wani lokaci domin hakan ne zai basu damar fahimtar halayen junansu. Domin maza na gajiya idan mace ta zamo mara sa nishadi, sai yaji rayuwar auran ya fitar masa a rai.

Karanta dalilin da yasa maza ke gajiya da matayansu

4.Yawan mita da naci: Idan mace ta zamo mai yawan mita ko naci na sa mazaje suji matayensu sun fita daga ransu har suji sun gaji domin rashin kwanciyar hankali.

Karanta dalilin da yasa maza ke gajiya da matayansu

5.Rashin kokari a shimfida: Mazaje na gajiya da aure idan matar ta kasance bata iya biya masu bukata yadda ya kamata ta fannin auratayya.

Karanta dalilin da yasa maza ke gajiya da matayansu

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng