Manyan labarai daga jaridun Najeriya

Manyan labarai daga jaridun Najeriya

Manyan labarai da suka yi fice daga jaridun Najeriya a yau Alhamis 4 ga watan Augusta

Jaridar This Day ta ruwaito cewa, sojoji basu damu da sabon chanjin shugaban kungiyar Boko Haram da kungiyar tayi ba. A jiya gidan radiyon BBC ta ruwaito cewa kungiyar musulunci wato Islamic State ta bayyana sabon shugaban kungiyar mai suna Abu Musab al-Barnawi wanda ya kasance mai Magana da yawun Boko Haram a da. Ya maye gurbin Abubakar Shekau.

Bisa ga jaridar Nigerian Tribune, ta ruwaito inda, tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya kai ziyara ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara a fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya a ranar Laraba, 3 ga watan Augusta, cewa babu wani madadin Najeriya guda.

Daga jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), ya ce shugabancin kasa da yayi a shekara ta 1966 ya zo mai a bazata domin shi baida burin mulkan kasa a lokacin, ya fadi hakan ne a jiya Laraba 3 ga watan Augusta, a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA KUMA: Yan Najeriya sun dawo kan Fayose kan tafiyar Aisha Buhari Amurka

Daga karshe jaridar Leadership ta ruwaito cewa, Kungiyar nan na BringBackOurGirls (BBOG) sun bayyana cewa sun sha alwashin tsaya way an matan Chibok kuma zasu ci gaba da tsaya masu har sai an ceto yan matan. Sunyi Magana ne a taron cikar yan matan kwanaki 840 da sace su.

Shugaban kungiyar Aisha Yesufu ta bayyana cewa kungiyar zata ci gaba a matsayin muryan yan matan kuma bazata gaza ba kamar yanda ta dauki alkawari. Ta kuma ce duk da yan matan sun dade a hannun yan kungiyar Boko Haram kungiyar taba cire rai da su ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng