An ga Ronaldo da sabuwar budurwar sa (kalli hotuna)
An ga Ronaldo da sabuwar budurwar sa (kalli hotuna)
Da alama Shahararren dan wasan kwallon kafar nan dan asalin kasar Portugal wanda kuma yake taka leda a kungiyar Real Madrid Cristiano Ronald ya yi sabuwar budurwa.
An dai ga shahararren dan wasan ne tare da budurwar tasa a garin Miami dake kasar Amuruka inda yake shakatawa. A wasu hotunan da suka watsu a kafafen sadarwa ta zamani, suna nuna shi ne tare da sabuwar budurwar tasa Cassandre Davis a cikin rana suna makale da juna.
Haka ma dai an ruwaito cewa an ga shahararren dan wasan tare da Davis din a wurin wani cin abincin dare na Seaspice. Ita dai sabuwar budurwar tasa tana sana'ar kawa da kwalliya ne da kuma kasuwa. Har yanzu dai babu wata magana tsayayya daga gare su din game da alakar dake tsakanin su. Abaya ma dai an ga Ronaldo da wata mai suna Eiza Gonzalez a wata ranar laraba amma daga baya sai makusan tan ta sun karyata labarin.
Asali: Legit.ng