Babban Limamin Masallacin Madina zai Ziyarci Abuja.  

Babban Limamin Masallacin Madina zai Ziyarci Abuja.  

 -Babban Liman Na Massalacin Annabi SAW Ze Ziyarci Najeriya.                                    

-Malamin Addini Sheikh Salah Bn Muhammad Al-Budair Ze Sauka Abuja Ranar Laraba 3,Agusta.

Ana tsammanin limamin massalacin Annabi SAW na garin Madina kasar Saudiya ya iso Abuja gobe 3,Agusta. Jaridar Daily post tayi rohoton cewa babban malamin zeyi kwana 3 yayin ziyarar shi. Al Budair wanda yana cikin fitattun masana Al-qur'ani a duniya ze bada sallar juma'a a babban masallacin kasar nan dake Abuja 5,Agusta 2016.

Babban Limamin Masallacin Madina zai Ziyarci Abuja.  

Bugu da kari an tsara cewa limamin ze bada Sallar Magriba da Isha'I a Babban masallacin na kasa da ke Abuja 3,Agusta,da kuma ranar Alhamis ze bada Sallar Asuba, da yamma kuma ze bada Sallar magriba da Isha'I a masallacin Annur da ke Wuse 2 Abuja. Mamban kwamitin tsare-tsare na ziyarar da shugaba 1 Ummah Abubakar Mahmud sunce "Babban limamin Salah bn Muhammad Al-Budair ze gana da yan Najeriya a wani Wurin da aka kebe.

Ziyarar Al-Budair din tazo yayin da ake ta rade-raden cewa ana kulle-kullen maida Najeriya kasar Musulunci. Bada dadewa ba Kungiyar masu rubutu ta kungiyar masu kare hakkin dan adam (HURIWA) suna ganin laifin shugaba Buhari dan mai da Najeriya kasar musulunci. Wata kungiya sun dauki cewa ministan harkokin gida Aldul-rahaman Danbazau ya tsallake dokar kundin tsarin kasa,ya anshi doka daga shugaban kungiyar addini Sarkin Musulmi na kara hutun karamar Sallah daga kwana 2 zuwa kwana 3. Daily Post ta kara bayyana cewaa (HURIWA) sun kara zargin gwamnatin Najeriya kan janyo rudani da matsala ga yan kasu da ma'aikatu masu zaman kansu na umurnin karayin Azimi 1 da ba'a shirya baa.

KU KARANTA : Aikin Hajjin bana : Saudiyya ta hana shiga da Goro

Kungiyar ta bayyana cewa kundin tsarin kasa ya tana da sashi na 10 wanda yace ba wani addini da za'a bi ra'ayinshi a kyale addini kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng