Wani mutumi ya lalata yarinya yar shekara 7 a cikin masallaci

Wani mutumi ya lalata yarinya yar shekara 7 a cikin masallaci

-An zargi Wani mutumi me shekaru 28 a duniya, Modiu Diallo, da laifin lalata wata yarinya me shekaru 7 a cikin wani masallaci a Surulere, dake jihar Lagas

-Mai shari’ar ya shaida wa kotu cewa zargin ya keta sashi na135 (2) da kuma 137 na kundin dokokin jihar Lagas, na shekara 2011

Wani mutumi ya lalata yarinya yar shekara 7 a cikin masallaci

Yan sanda sun gurfanar da wani mutumi mai shekaru 28 a duniya, Modiu Diallo, a gaban wani babban kotun Surulere, na jihar Lagas kan zargin ya lalata yarinya yar shekara 7 a wani masallaci. An gurfanar da wanda ake zargi a ranar Litinin 1 ga watan Yuli, ana zargin ya aikata laifin da misalign karfe 6 na safe a ranar 13 ga watan Yuli, a masallacin juma’ar Iponri, karamar hukumar Surulere, jihar Lagas, a cewar mai shari’a Sgt. Anthonia Osayande, News Agency of Nigeria (NAN) ce ta ruwaito.

Mai shari’ar ya bayyana wa kotu cewa zargin yak eta sashi na 132 (2) da kuma sashi na 137 na kundin dokokin jihar Lagas na shekara 2011.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya na shirin horar da yan boko haram 800

Duk da haka, a lokacin da aka karanto wa wanda ake zargi laifin da ake zargin sa da shi ya karyata laifin cewa bai aikata ba. Alkalin kotun, Mrs Ekpaye Nwachukwu, ta bayar da belin wanda ake tsaro naira 500,000 ta kuma daga sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Satimba .

A wata ci gaba, Limamun masallacin Annabi (SAW), dake birnin Madina, kasar Saudiya, Sheikh Salah Bin Muhammad Al-Budair zai zo babban birnin tarayya Abuja a gobe, 3 ga watan Augusta. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa babban malamin musuluncin zai yi tsawon kwanaki uku a ziyarar sa na watan Augusta.

A yayin ziyarar, Al-Budair, wanda ke daya daga cikin wadanda suka fi iya karatun Al-Qur’ani a duniya, zai jagoranci salar Juma’a a masalacin kasa baki daya dake babban birnin tarayya Abuja a ranar Juma’a 5 ga watan Augusta na shekara 2016.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng