Wani dan shekara 60 ya auri yar shekara 6
An kama wani mutum da shekara 60 a kasar Afghanistan ta dalilin auren yarinya yar shekara 6.
Jaridar India Today ta bada rahoton cewa, Mohammad ya bayyana dalilin da yasa ya auri yarinya cewa addinin shi ne kune iyayen ta suka bashi. Amma, da aka tuntubi iyayenta, sun ce anyi garkuwa da ita ne a herat akan bodan iran kuma basu solan komai akan auren ba.
Karim ya bayyana cewa shi bai aure yariyar ba a boye, yace anyi a gaban mutane 50 a unguwar, Amma iyayenta sun musanta hakan. Game da wani jami'in ma'aikatan mata a ghor, tace yarinyan bata magana amma tana nanata cewa tana tsoron mutumin. A yanzu haka yarinyar na karkashin kulawan matan a garin Ghor.
KU KARANTA : Wani yayi fyade ma ‘yar Cocinsu.
Ofishin gwamnan tace iyayen yarinyar na hanyar su na zuwa dawo da ita gidansu. Amma mai magana da yawu gwamnan jihar ya tabbatar da cewan an kama mutumin kuma ana gudanar da bincike a kan al'amarin.
Asali: Legit.ng