Makauniyar yarinya ta shiga harkan karuwanci saboda wannan dalilin
Wata makauniyar yarinya, mai suna Kelly Chitungwiza, ta bayyana cewa ta shiga harkan karuwanci ne saboda ta samu kudin da za’ayi mata aiki a ido
Kelly ta bayyana wa H-Metro cewa tana so ta hada dalan 500 na Amurka wanda za’ayi mata aikin ido da shi,yayin da masoyinta, Elton ya bada tabbacin tsaronta saboda karda abokan sana’arta suyi amfani da magantar ta gurin cutar da ita. Kelly ta fito dga Mudzi inda yawancin yanuwan ta suke MM sun dade da hanata ziyartar su.
Elton ya ce: “ina lura da wandanda suke tare da Kelly saboda tsaro, kuma ina tabbatar da cewa bata kamu da sanyi ba ta hanyan hada mata garwashi.”
Kelly ta bayyana halin da take ciki:
“Rayuwata ta kasance ba kamar da ba bayan da mahaifiyata ta mutu, kuma yayana ne ya tilastani shiga harkan karuwanci. Banida matsalar muhalli tunda ina hayar wani daki tare da saurayina Elton a Unit K Chitungwiza kuma shi ke ajiye mun kudin da nake samu daga gurin mazan da nake biyawa bukatun su ta hanyar karuwanci. An yada a shafin sadarwa na Facebook da Twitter.
KU KARANTA KUMA: Dangote ya sauka daga jerin manyan masu kudi 100
“Elton na tabbatar da cewa ya dauki lamban duk motan wanda ke dauka na ya kuma tabbatar da cewa ban shiga mugun hannu ba. Ina zama a Epworth kafin na dawo Chitungwiza tare da saurayina.
“Bayan na gama hada kudin bazan ci gaba da karuwanci ba saboda rayuwa bata yi mun kyau ba kwatakwata da kuma wasu mazajen da ke amfani da makanta ta gurin bani kudi kadan. Ba haya mai kyau bane na hada kudi amma bani da wani zabi da ya wuce wannan. Idan na samu wani da zai taimaka mun bazan ci gaba da yawo a titi ba."
Asali: Legit.ng