Dangote ya sauka daga jerin manyan masu kudi 100
-Mai kudin Afrika, Aliko Dangote ya sauka daga jerin masu kudin duniya 100
-Dangote na da kimanin dala billiyan 15.4 (naira trilliyan 3.05) a watan Maris, yanzu ya koma Dala billiyan 11.1 (naira trilliyan 3.3) wanna ne dalilin da ya yasa ya kasance ya kudi a naira, amma ya talauce a Dala
Mai kudin Najeriya da Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya sauka daga cikin jerin masu kudin duniya 100.
Faduwar Dangote ya faru ne sakamakon faduwar naira.
A cewar Bloomberg, Alhaji Aliko Dangote wanda ya kasance mutun na 51 a masu kudin duniya a watan Maris na shekara 2016, ya sauka a yanzu zuwa lamba 101.
Kamfanin Dangote cement, daya daga cikin manyan hannun jarin Dangote a Najeriya, ya kasance kamfani mafi girma a kamfanin da ba mallakin gwamnati ba a Najeriya, kuma wanda suka fi samar da ciminti a yakin sahara Afrika.
A halin yanzu gidauniyar Dangote tayi alkawarin kuma gina hukumomin lafiya da mayakan Boko Haram suka lalata, musamman wadanda aka lalata a karamar hukumar Gujba da Gulani na jihar Yobe.
KU KARANTA KUMA: labarai daga jaridun Najeriya
Dangote na da kimanin dala billiyan 15.4 (naira trilliyan 3.05) a watan Maris, yanzu ya koma Dala billiyan 11.1 (naira trilliyan 3.3) wanna ne dalilin da ya yasa ya kasance ya kudi a naira, amma ya talauce a Dala.
Duk da haka, Dangote yafi Donald Trump kudi, Billonoiyan Amurka kuma dan takarar shugabancin kasa, da kuma Oprah Winfey, mai gidan talabijin din US TV, ta biyu a cikin mata masu kudi a bakar fata na duniya. An kimanta cewa Trump da Oprah na da dala billiyan 4.5 da dala billiyan 3.1.
Kamfanin Dangote cement, daya daga cikin manyan hannun jarin Dangote a Najeriya, ya kasance kamfani mafi girma a kamfanin da ba mallakin gwamnati ba a Najeriya, kuma wanda suka fi samar da ciminti a yakin sahara Afrika.
A halin yanzu gidauniyar Dangote tayi alkawarin kuma gina hukumomin lafiya da mayakan Boko Haram suka lalata, musamman wadanda aka lalata a karamar hukumar Gujba da Gulani na jihar Yobe.
Asali: Legit.ng