labarai daga jaridun Najeriya
Labarai daga jaridun Najeriya a yau Litinin, 25 ga watan Yuli
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, gwamnatin tarayya na shirin gurfanar da mambobi 9 daga cikin 26 na majalisar jihar Ekiti kan zargin jabun takardan sakamako na makarantar su. Wata majiyar tsaro ta shaida wa daya daga cikin wakilanmu a Abuja a ranar Lahadi cewa an yanke shawarar gurfanar da su bisa ga hujja da aka samu daga wani bincike da hukumar DSS tayi kan takardun makarantar yan majalisar jihar.
Hukumar DSS, ta tattaro cewa, tayi bincike kan takardun sakamako da yan siyasan suka ba hukumar zabe ta kasa a lokacin zaben shekarar bara.
Jaridar Daily Trust ta rubuto cewa, an fara samun rikici a jam’iyyar All Progressive Congress (APC) babin jihar Adamawa bayan dawowar Mallam Nuhu Ribadu da Marcus Gundiri jam’iyyar. Sanarwan da shugaban ma’aikatan Gwamna Muhammadu Jibrilla, Abdurrahman Abba Jimeta yayi, na sukar yunkurin ne ya yi sanadiyar faruwan rikicin.
An bayyana cewa, wasu daga cikin jigajigan jam’iyyar sun ce sunyi mamakin dalilin da ya sa aka bar Ribadu ya dawo jam’iyyar shekara daya bayan jam’iyyar ta kwace mulki daga hannun jam’iyyar PDP. A cewar jaridar The Nation, gwamnatin jihar Ondo ta fara shirinta, na rabon kayan abinci ga mata a kyauta,a yau a karamar hukumar Ose.
An shirya rabon kayan abinci ga mataye a hukumomi 18 da ke kewaye a jihar, kuma ana sa ran mataye 100,000 ne zasu amfana a jihar.
KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa Babangida ya cire ni daga kan mulki – Buhari
A cewar Jaridar Daily Times, Kungiyar tsagerun Niger Delta Avengers sun kai hari a wani bututun mai da ke mallakin Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) a jihar Akwa Ibom. Bisa ga Mudoch Agbinibo, kakakin kungiyar, an kai harin ne a karamar hukumar Nsit-Ibom, da misalign karfe 11:30 na ranar Lahadi.
Daga karshe Jaridar The Guardian ta bayyana cewa, tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, yay aba wa tsarin shugabancin kakakin majalisar wakila, Yakubu Dogara. An bayyana haka ne cikin wata sanarwa daga mai ba Dogara shawara na musamman kan harkokin labarai, Mr Turaki Hassan, a ranar Lahadi a babban birnin Tarayya Abuja. Hassan ya bayyana cewa Babangida ya fadi haka ne a lokacin da karbi bakoncin yan majalisar wakilai a gidansa na Hiltop dake garin Minna a ranar Lahadi.
Asali: Legit.ng