Jonathan tare da iyalin sa a filin jirgin sama na Abuja (hotuna)
An hangi Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan, tare da matarsa Patience da dansu a filin jirgin sama na Abuja a ranar Lahadi 24 ga watan Yuli.
Tsohon ministan harkokin sufurin sama, Osita Chidoka ne ya yada hotunan a shafin sadarwa na Twitter.
KU KARANTA KUMA: Kungiyoyin yan bindiga masu hatsari 5 daga Niger Delta
Mu tuna a makonni biyu da suka shige, Mr Jonathan wanda ya sauka a filin jirgin Port Harcourt international airport tare da matar sa, Dame Patience Jonathan sun samu tarba daga gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike da wasu jam’ian gwamnati.
Haka kuma, lokacin da Goodluck Ebele Jonathan baya kasar, jam’iyyar sa, Peoples Democratic Party (PDP) ta kasance cikin matsala kan wanda zai shugabanci jam’iyyar.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) suna binciken yanda aka yi almubazaranci da dukiyan kasa, a na kuma binciken yan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) wadanda ke da nasaba da abun.
A wata zantawa da jaridar Vanguard, Lawal ya nace kan cewa jam’iyyar PDP da ta kasance a kan mulki na tsawon shekaru 16, ya ba mambobin jam’iyyar dama a kan kudin kasa wanda wannan ne dalilin da ya sa a ke binciken cin hanci da rashawa a kansu.
Asali: Legit.ng