Dalilin da yasa Babangida ya cire ni daga kan mulki - Buhari

Dalilin da yasa Babangida ya cire ni daga kan mulki - Buhari

-Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce an cire shi daga kan mulki a shekara ta 1985 saboda yana shirin  kawar da sojojin da ke cin hanci da rashawa

-Shugaban kasa ya kuma bayyana cewa tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida da kuma Janar Aliyu Gusau, ne suka cire shi domin su ceci kansu

-Ya kalubalance su da su fadi gaskiya a kan dalilin da yasa sukayi mai juyin mulki          

Dalilin da yasa Babangida ya cire ni daga kan mulki - Buhari

An cire shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari daga kan mulki, shekaru 31 da suka wuce, saboda yana shirin kawar da sojojin da ke aikata cin hanci da rashawa.

Buhari, wanda bai kare sojoji ba cikin yaki da cin hanci da rashawar sa da ke gudana, ya ce babban shugaban sojoji, kargashin jagorancin tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida da Janar Aliyu Gusau, sun cire shi a watan Augusta na shekara 1985, domin su kare kansu daga fushin.

A wata zantawa da jaridar Interview Magazine, Buhari ya kalubalanci Babangida da Gusau da su fadi gaskiyar dalilin da yasa sukayi masa juyin mulki.

KU KARANTA KUMA: Ministan Labarai da al’adu ya ziyarci hedkwatar BBC

Buhari ya zama shugaban kasar Najeriya a ranar 31 ga watan Disamba, a shekara ta 1983, bayan shi da magoya bayan sa sun hambarar da gwamnatin Shehu Shagari.

Haka zalika, a ranar 27 ga watan Augusta, ta shekara 1985, mulkin shugaban kasa Buhari ya kare sakamakon juyin mulki daga shugaban sojoji, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), wanda ya kasance daga cikin tawagar Buhari kuma wanda ya asasa juyin mulkin shekara ta 1985.

Shugaban kasa ya bayyana cewa ya san Babangida na shirin yi masa juyin mulki. Sun tattauna tare da shi a ofishin sa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng