Manyan labarai daga jaridun Najeriya

Manyan labarai daga jaridun Najeriya

Manyan labarai kan abubuwan da ke faruwa daga jaridun Najeriya a yau Juma’a 22 ga watan Yuli

Jaridar Daily Sun ta ruwaito cewa sojojin Najeriya sun kashe yan kungiyar Boko Haram 42, a lokacin wani hari da suka kai a jiya Alhamis 21 ga watan Yuli, a kauyen Garere, karamar hukumar Kukawa na jihar Borno. Bisa ga kakakin sojojin, Col. Sani Usman, sun ceto mutane 80, wanda ya hada da mataye 38, da yara 42 a lokacin harin.

Manyan labarai daga jaridun Najeriya

A jaridar Vanguard kuma, munji cewa, shugaban majalisar Dattawa, Dr Bukola Saraki, karyata cewa da akeyi ya koma jam’iyyar PDP. Ya ce yana nan a jam’iyyarsa ta All Progressive Congress (APC). Saraki y aba da tabbacin ne don mayar da martani ga rahotannin da kafofin watsa labarai sukayi na cewa ya bar jam’iyyarsa zuwa jam’iyyar PDP. Yayi maganan ne a jiya, Alhamis 21 ga watan Yuli.

Bisa ga jaridar The Nation,mun gano rahoto, cewa: Yan Najeriya sunji labara mara dadi a jiya, na koma bayan tattalin arziki. Amma ministan kudi, Mrs Kemi Adeosun ta bayyana cewa baa bun tashin hankali bane, domin ba abune mai dorewa ba.

KU KARANTA KUMA: Buhari zaya sasanta da yan bindigan niger delta

Mrs Adeosun ta bayyana koma bayan tattalin arzikin ga sanatoci,a lokacin da take basu bayani kan yanda za’a shawo kan matsalar.

Daga karshe, Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na kan tattaunawa da tsagerun Mayakan Niger Delta a yanzu, domin kawo karshen hare-haren da ake wa guraren samar da man petir a yankin.

Ya bayyana cewa ana tattaunawar ne ta hanyar kampanonin mai, da masu zantarwa, kuma ana sa ran kawo karshen matsalar tsaro mai dorewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel