Ko sanko ne ke shirin kama Dan wasa Gareth Bale?

Ko sanko ne ke shirin kama Dan wasa Gareth Bale?

LABARIN WASANNI

KO SANKO NE KE SHIRIN KAMA DAN WASA GARETH BALE?

Ko sanko ne ke shirin kama Dan wasa Gareth Bale?

 

 

 

 

 

Da alamu kwana-kwanan nan Gareth Bale zai yi sanko; domin gashin kan sa na gwaguyewa.

Da alamu cewa sanko na neman cin kan dan wasan gaban Real Madrid na Kasar Wales. Sababbin hotunan dan wasan suna nuna cewa sumar sa ta kai na cinyewa a hankali. Hotunan tsohon dan wasan na Tottenham Hotspurs dai suna bayyana cewa gashin san a kai na a ta cinyewa kadan-kadan. Sai dai wajen dan kwallon kafa, musamman irin su Gareth Bale, sun yarda da kwalliya da ado. Yan wasa irin su Bale bas u wasa da aski ko gyaran gashi; sai ka ga kowa yayi irin na sa salo. A wajen irin wadannan ‘yan wasa, da kwalliyar su da takalmin kwallon su, kusan duk abu daya ne. Kwalliyar ta hada daga rigar jikin su har gashin da ke bisa kan su.

A SAUKE MANHAJAR MU NA Legit.ng DOMIN SAMUN LABARIN WASSANNI.

An dai lura da gwaguyewar dan wasan tun shekarar sa ta farko a Kungiyar Real Madrid, bayan ya taso daga Tottenham Hotspurs ta Ingila. Masu shegen sa ido ne suka lura da hakan. Haka nan kuma duk da irin kokarin da yi ma Kasar sa ta Wales a Gasar EURO 2016; Gasar Zakarun Kwallon Kafa ta Nahiyar Turai da aka buga wannan shekara ta 2016 a Kasar Faransa, sumar gashin kan Gareth Bale din ta zama abin magana ga jama’a. Hotuna daga Gasar EURO 2016 din na Faransa dai suna bayyana cewa sumar Bale na ta cinyewa ta tsakiya.

A wani wasan da dan gaban Kungiyar Real Madrid ya buga wancan shekarar tsakanin su (Real Madrid) da Real Sociedad, sankon na Gareth Bale ya fito karara, har kowa ya gani, aka yi ta magana.

KU KARANTA: AN FITAR DA TSARIN BIZNE STEPHEN KESHI

 

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: