Jihohin da rikicin addini ya afku a Najeriya
-Jihohi bakwai da rikicin addini ka iya afkuwa
-Yan leken asiri sun ce Shugaban kasa Buhari kar ya dauki barazanar da wasa
Nan da sannu rikicin addini mai tsanani na iya afkuwa a kasar Najeriya idan ba’a mayar da hankali ga rahotanni da yan leken asirin al’umman Najeriya ke kawo ba. A cewar wata majiya da jaridar Sahara Reporters ta samo, an motsa rikicin ne a siyasance, domin girgiza hadin kan kasa, ta hanyar farfado da kisan kiristoci da musulmai sukayi a arewa kwanaki.
Jihohin da aka lissafa sun hada da: Babban birnin tarayya, Abuja, jihar Niger, jihar Kaduna, Jihar Kano, Jihar Nasarawa, Jihar Plateau, da kuma jihar Benue. Majiyar sun kuma bayyana cewa yawan makamai da aka gano a muhimman unguwannin Abuja da sauran jihohi shiddan ya isa dalili da zai sa gwamnatin tarayya karta dauki barazanar da wasa.
KU KARANTA KUMA: Harin makiyaya yafi karfin shugaba Buhari
An kuma samo rahoto cewa wadannan ne kashe-kashen addini da kabila da akayi amfani dashi gurin cimma wadannan yunkuri da ake shirin yi.
. Kisan da akayi a ranar 29 ga watan Mayu a jihar Niger na wani mutun mai shekaru 24 da jami’an tsaro uku;
. Kisan wata matar fasto a akayi a jihar Kano, a ranar 2 ga watan Yuni;
. Harin da aka kai wa wani mutun a Jihar Kaduna kan ya ci abinci a watan azumi; da kuma
. Kisan wata mace mai da’awar addinin kirista a Abuja, a ranar 9 ga watan Yuli. Wadan nan ne da hujjar da ake so ayi amfani da.
Asali: Legit.ng