Chelsea na neman Dan wasan Kungiyar AC Milan
– Kungiyar Chelsea na neman Diego Lopez na AC Milan
– Lopez zai zama mataimakin Golan Chelsea Thibaut Courtois
– Asmir Begovic na Chelsea zai koma Kungiyar Everton.
Kungiyar Chelsea ta Ingila na zawarcin Golan Kungiyar AC Milan ta Kasar Italiya cewar dillalin dan wasan da ke tsaron raga, Lopez Diego. Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa sabon kocin Kungiyar Chelsea ta Ingila, Antonio Conte na kokarin sayen Golan AC Milan a matsayin wanda zai maye gurbin Golan Kungiyar Chelsea Asmir Begovic, wanda ke shirin komawa Kungiyar Everton. Antonio Conte yana neman dan wasan da ke tsaron ragar mai shekaru 34 da haihuwa duniya.
A SAUKE MANHAJAR MU NA Legit.ng DOMIN SAMUN LABARAN WASANNI.
Tsohon dan wasan na Real Madrid, Diego Lopez bai samu buga wasanni ba a gasar wancan shekarar saboda rauni. Dan wasa Diego Lopez ya buga wasanni 9 ne kacal a AC Milan a bara dalilin rashin lafiya. Sandaiyyar haka ne dai tsohon Golan na Kungiyar Real Madrid ta Spain ya rasa wurin sa ga wani matashin gola dan shekaru 17 mai suna Gianluigi Donnarumma. Yanzu, babu mamaki idan har Diego Lopez din ya bar AC Milan ya koma Kungiyar Chelsea da ke Ingila.
KU KARANTA: DAN WASA BAI KOMA JUVENTUS DAGA NAPOLI.
Manuel Garcia Quilon wanda shine dillalin dan wasan, ya fada ma kafar Calciomercato cewa Kungiyar Chelsea tana zawarcin dan wasan na AC Milan, yace duk da dai ba su kare magana ba, amma dai maganar tayi karfi sosai. Kawo war haka dai Kungiyar Chelsea ta saye yan wasa da suka hada da Michy Batshuayi daga Marseille, da kuma N’golo Kante daga Leicester a kakar sayayyan wannan shekara.
A SAUKE MANHAJAR MU NA Legit.ng DOMIN SAMUN LABARAN WASANNI.
Asali: Legit.ng