Dan wasan kwallon Real Madrid ya rangada waka
– Dan wasan Real Madrid, Jese Rodriguez ya saki bidiyon wakar sa.
– Dan wasan dai da ya rikide ‘Jey M’ ya rangada wata sabuwar waka.
– Bidiyon na dauke da mutane irin su: Alexis, Fido, da De La Ghetto
Dan wasan kwallon kafan Real Madrid ya fitar da wani kundin wakar da ya rangada a bidiyo. Dan wasan mai buga gaba a Real Madrid tare da su Karim Benzema, Cristiano Ronaldo, da Gareth Bale ya nuna ba a fili kadai yake da kwarewa ba. Dan wasan ya fito a matsayin mawaki JEY M a sabon bidiyon wakar sa.
Jese R., yayi wata waka mai suna Yo Sabia da yaren Kasar Spain (Ma’anar wakar dai, iya sani na). A bidiyon za a ga abokan yan wasan da suka hada da: Alexis, Fido, De La Ghetto da Carlitos.
A SAUKE MANHAJAR MU Legit.ng DOMIN SAMUN LABARIN WASANNI.
Me ku ke gani game da Jese? Shin ko zai koma fagen wake-wake ne idan kwallo ta ki ya a Real Madrid din? Ko kuwa?
KU KARANTA: KO KA JI AIKIN DA HENRY YAKE NEMA?
Asali: Legit.ng