Kowanne tsintu kukan gidansu yake - Omokri
KOWANE TSUNTSU KUKAN GIDAN SU YAKE YI-INJI RENO OMOKRI
Reno Omokri, wani mai ba tsohon Shugaban Kasar Najeriya Jonathan Goodluck shawara ya shawarci mutanen Kasar na Najeriya. Reno Omokri, tsohon mai bada shawara ga Shugaban Kasar Najeriya kan harkokin yada labarai (ta kafafen zamani) ya kira ‘yan Najeriya da suyi irin kukan gidan su a ko ina suke a fadin duniyar nan.
Reno Omokri, wanda babban limamin cocin kirista ne, wanda asali shine ya bude cocin ‘Mind of Christ Christian Center’ da ke California, ta Kasar Amurka, ya yi wannan jawabi ne ta shafin sa na Facebook a ranar Laraba 13 ga wannan watan na Yuli ga ‘Yan Najeriya akan Nahiyar su ta Afrika. Reno Omokri yake magana kan yadda mutanen Afrika, bakaken fata ke kokarin rikidewa suna kwaikwayon turawa, fararen fata da sunan ci gaba ko wayewar zamani. Reno Omokri dai yace kowane tsuntsu kukan gidan su yake yi.
KU KARANTA: SHUGABA BUHARI YA KADDAMAR DA WATA TAWAGAR SOJI
Karanta abin da Fasto Reno Omokri yake fada (A nan kasa):
“Ka da mutum ya kuskura ya sake, ya bar Kasar sa ta Najeriya ya koma Kasashen yammacin duniya ya tare, har ya canza sunan sa. Idan har Amurka ta na iya zaben mutum kamar Barack Obama a matsayin Shugaban kasa, ba ka da hujjar canza naka suna. Ina dalilin ‘Emeka’ ya koma ‘Mike’, ko ‘Kayode’ ya dawo ‘Kay’, ko a kira ‘Haruna’ da ‘Harry’. Idan ka girmama kan ka, sai duniya ta girmama ka, a ko in aka shiga.”
Gidan labarai na BBC da ke London sun bayyana Reno Omokri a matsayin fitaccen mai watsa labarai, shi ke gabatar da shirin nan da aka sani na ‘Transformations With Reno Omokri’, wani shiri ne na mabiya addinin kirista da ake gabatarwa a birnin San Francisco na Kasar Amerika. Har wa yau, Fasto Reno ya buga littafai da dama wadanda suka hada da: Shunpiking: No Shortcuts to God, da Why Jesus Wept, duk na addinin kirista. Reno Omokri, yana daya daga cikin masu magana da yawun-bakin tsohon Shugaban Kasar Najeriya, Jonathan Goodluck, yayi kokari wajen kawo sauyin amfani da kafafen yada labaran zamani wajen manufar siyasa.
Asali: Legit.ng