Amurka tayi magana game da Aisha Buhari
Amerika tayi magana game da zargin da Fayose yayi ga Aisha Buhari.
– Makonni 3 da suka wuce, Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya zargi Aisha Buhari cikin wata tafkekeiyar badakala, Amerika sun fitar da jawabi dangane da wannan.
– Amerika ta bada martini game da zargin da aka yi ma Aisha Buhari, wannan dai zai kawo karshen ce-ce-ku-cen da aka yi tayi a kwanakin nan.
Amurka ta maida martini ga Gwamnan Jihar Ekitin Najeriya Ayo Fayose cewa babu wani laifi da aka taba kama matar Shugaban Kasar Najeriya, Aisha Buhari da shi a kasar. Kasar Amurkar kuma ta kara da bayyana cewa, babu wanda ke neman Aisha Buhari a kasar da sunan wani laifi.
A ranar 20 ga watan Yunin wannan shekaran ne Ayo Fayose na jihar Ekiti ya fitar da wasu takardu daga ma’aikatar Shari’a ta Kasar Amurka da ke zargin wata Aisha Buhari da laifin tura wasu makudan kudi zuwa ga wani tsohon mai laifi da aka sani da William Jefferson. Jaridar Punch ta rahoto cewa wani jami’in Amurkan mai suna Frank Sellin ya karyata wannan zargi na Ayo Fayose ta wani sakon email da aka tura masa. Da Mr. Sellin ya ke bada amsa ga tambayar da aka yi masa dangane da zargin Aisha Buhari da tura makudan kudi har Miliyan $185 a sananniyar badakalar da aka fi sani da ‘Halliburton’, sai yake cewa ba su san da wannan batu ba.
KU KARANTA: ZAHRA DA YUSUF BUHARI SUN KAMMALA KARATU
Ayo Fayose dai ya ba mutane mamaki lokacin da ya bayyana cewa ana neman matar Shugaban Kasar Najeriyar, Aisha Buhari a Amurka saboda wani laifin da ta aikata. Fayose na Jihar Ekiti yace: “Ko shi (Shugaban Kasan) ai ba mala’ika bane. Muna da labarin katafaren ginin da yayi a Abuja. Mai dakin sa (Aisha Buhari) tana da hannu cikin badakalar ‘Halliburton’. Lokacin da aka daure Mista Jefferson na Kasar Amurka, Aisha Buhari ta tura kudi har dala $170,000 gare sa. Sunan ta nan a shafi na 25 na takardun, jama’a su duba za su gan ta…” Inji Ayo Peter Fayose na Jihar Ekiti.
Asali: Legit.ng