Tauraron Real-Madrid yace ba zai tafi Arsenal ba

Tauraron Real-Madrid yace ba zai tafi Arsenal ba

Tauraron Real-Madrid yace ba zai tafi Arsenal ba

– Morata ya dawo gida, Real-Madrid

– Kulob din Arsenal na neman dan wasan

– Morata na so ya zauna a Real-Madrid

Tauraron Real-Madrid yace ba zai tafi Arsenal ba
Yan wasan Real madrid

Goal.com sun rahoto cewa Kungiyar Real-Madrid ba za ta cigaba da tattaunawa da Kungiyar Arsenal ba danagane cinikin dan wasan gaban ta, Alvaro Morata. Wani babban Jami’in kulob din Juventus, Beppe Moratta ya sanar da cewa Alvaro Morata zai koma kungiyar sa ta asali, Real-Madrid a kakan bana kan kudi fam miliyan 23 na dalar EURO. Dan wasan dai ya bar Real Madrid ne zuwa Juventus shekaru 2 da suka wuce. Yanzu haka Real-Madrid din ta nemi dan wasan na ta ya dawo gida bisa wata yarjejeniya da aka kulla a baya. Wata majiya daga DON BALON ta bayyana cewa Zidane na iya saida Dan wasa Morata kan farashi fam miliyan 30, hakan zai sa Real-Madrid din ta samu riba kan cinikin ta.

KU KARANTA: KULOB DIN BARCELONA TA SAYI WANI DAN WASA.

Sai dai Goal sun rahoto cewa yanzu haka tattaunawar tsakanin Real-Madrid da Arsenal ya tsaya, domin Kungiyar Real-Madrid din sun saka ma dan wasan nata suna kan fam miliyan €75. Idan dai har aka saye Alvaro Morata da wannan kudi, zai shiga tarihi a Birtaniya. Alvaro Morata dai ne ya buga ma Kasar sa ta Spain lamba 9 a Gasar zakarun Nahiyar Turai na EURO da aka buga wannan shekarar ta 2016 a kasar Faransa, inda har ya ci kwallaye. Morata ya dai ci kwallaye 27 cikin wasanni 93 da ya buga. Dan wasan dai ya buga a Real-Madrid, sannan ya koma Juventus inda ya shekara 2 kafin ya dawo Real-Madrid din a bana.

A SAUKE MANHAJAR MU NA Legit.ng DOMIN SAMUN LABARIN WASANNI.

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: