Hukumar JAMB ta fitar da sabon tsarin shiga makarantu na gaba da Sakandare

Hukumar JAMB ta fitar da sabon tsarin shiga makarantu na gaba da Sakandare

Hukumar JAMB ta fitar da sabon tsarin shiga makarantu na gaba da Sakandare.

– JAMB tace rahoton da aka yi ta yadawa a baya, ba gaskiya bane.

– Hukumar Jarrabawa ta JAMB ta fitar da ka’idoji 3 da ake bukata wajen samun shiga makarantu na gaba da Sakandare.

Wani Jam’in hukumar, shugaban masu kula da harkokin watsa labarai, Fabian Benjamin yayi wannan jawabi mai dauke da ainihin matakan ka’idojin da ake bukata domin zuwa makarantu na gaba da sakandare a wannan Shekara ta 2016. A baya dai hukumar jarrabawar ta JAMB ta bayyana cewa za a kawo sabon tsari na shiga Jami’o’i da suaran makarantu.

Hukumar JAMB ta fitar da sabon tsarin shiga makarantu na gaba da Sakandare

 

 

 

 

 

Kamar dai yadda labarin ya zo mana daga hukumar yada labarai na kasa (NAN) a ranar Lahadi nan, hukumar dai ta ayyana cewa za a bi ka’idoji 3 ne wajen zuwa makarantu na gaba da sakandare, wanda sune; Cancanta, yankin da makarantun suke, da kuma duba da bangaren da ke fama da karancin ilmi. Hukumar dai tayi wannan bayani ne a karshen makon nan, a garin Legas.

Ga dai cikakken bayanin da JAMB tayi:

“Bayan taron kara ma juna sani da aka gudanar karkashin Minastan Ilmi na Kasa game da hanyoyin zuwa makarantu na gaba da Sakandare na wannan Shekarar ta 2016. Gwamnatin Tarayyar kasar ta amince da matakan shiga makarantun da doka ta kafa. Wannan dai ya biyo bayan soke jarabawar ‘POST-UTME’ da Gwamnatin Tarayyar tayi. Ba za ayi amfani da wani tsari na maki ba, kamar yadda aka yi ta yadawa a kafafen labarai. Tsarin makin da ake magana, kawai kwatance ne ake yin a yadda wasu jami’o’i ke daukar daliban su, yayin da wasu kuma suke kara yin wani gwaji bayan nan (PUTME). Ganin haka ne, kafafen yada labarai suka yi tunanin wannan ne matakin da za a bi wajen samun shiga makarantu na gaba da sakandare”

Hukumar kuma ta bayyana cewa ana bukatar takardun shaidar SSCE na WAEC, NECO, NBTE ko kuma ALevel wajen tantance dalibai. Za a bukaci mataki na ‘Credit’ a bangaren Turanci da Lissafi da kuma sauran abin da ya danganci abin da dalibi yake so ya karanta. Sai dai Kungiyar Malaman Jami’o’i na Kasar watau ASUU, abin bai yi mata dadi ba.

KU KARANTA: AN SACE KAYAN TALLAFIN ABINCI NA MASU GUDUN HIJIRA

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: