Shugaban Kasar Argentina ya maganta kan ritayar Messi

Shugaban Kasar Argentina ya maganta kan ritayar Messi

Shugaban Kasar Argentina yayi magana game da ritayar Lionel Messi.

– Shugaban Kasar Argentina ya bayyana tattaunawar sa da Messi.

– Shugaban Kasar na da tabbacin cewa dan wasan ba zai ajiye kwallon ba

Shugaban Kasar Argentina ya maganta kan ritayar Messi
Mess

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Mista Mauricio Marci na Kasar Argentina yace yana mai tabbacin cewa dan kwallon duniya Lionel Messi ba zai ajiye kwallo a Kasar sa ba tukun. Shugaban Kasar yace ba sa da shakkar cewa Messi zai kara taka ma Kasar Argentina leda. Shi kyaftin din Kasar Argentina Lionel Messi, yace shi da buga ma Kasar sa kwallo kuma sai a lahira! Ya dai sha wannan alwashin ne yayin da ya rasa kofin gasar Nahiyar Amurka watau COPA AMERICA.

A sauke manhajar mu, domin samun labarum wasanni.

Bayan an doke kasar Argentina a Gasar COPA AMERICA, kofin zakarun Nahiyar Kudancin Amurka, Lionel Messi yace fau-fau, shi da kara buga ma Kasar sa ta Argentina kwallo, bayan ya ga ya rasa wasannin karshe ‘finals’ dai-daya har hudu. Messi dai yace, ba shi da rabo, kuma yayi Alan-baran cewa ba shi, ba bugawa Argentina. Ya yanke shawara, ta kare, tun da ya zubar da bugun finaritin sa. Sai dai duk da haka, masoya dan wasan da ma wasu ‘yan kwallon; na da da na yanzu, suna ta rokon dan wasan da ya taimaka ya sake shawara. Shugaban Kasar ta sa ta Argentina, Marci na daga cikin masu wannan roko.

A baya shugaban Kasar yace: ya kira sa ya masa murnar kokarin da suka yi a Gasar, abin farin cikin mu ne da murna ace zakaran duniya. Mista Mauricio Marci ya bayyana cewa yayi magana da dan wasan, yana da kuma tabbacin zai dawo buga ma Kasar sa. Mista Marci, shugaban Kasar Argentina yace: “Nayi magana da shi a waya, na tabbata zai dawo. Duniya babu kamar sa!” Ko a makon nan Cristiano Ronaldo yayi magana game da ritayar dan wasan Lionel Messi.

KU KARANTA: TORRES ZAI CIGABA DA TAKA LEDA A ATHLETICO MADRID

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel