Ronaldo yayi magana game da ritayar Lionel Messi

Ronaldo yayi magana game da ritayar Lionel Messi

Ronaldo yayi magana game da ritayar Lionel Messi

– Messi ya ajiye Kwallo a Kasar sa ta Argentina

– Dan wasan Kasar Argentina bai kara magana ba tun bayan lokacin

– Ronaldo yayi magana game da batun

Ronaldo yayi magana game da ritayar Lionel Messi

 

 

 

 

 

Tsohon dan wasan Kasar Brazil, Ronaldo De Lima yayi magana dangane da ritayar dan wasa Lionel Messi na Argentina. Gwarzon ya kira Messi da ya janye maganar ajiye kwallo. Kyaftin din dai na Argentina, Lionel Messi yace ya gama buga ma gida wasa ne bayan da ya sha kashi a wasan karshe na gasar zakarun Nahiyar Amurka watau COPA AMERICA. Kasar Argentinar Messi dai ta kara shan kayi ne hannun Kasar Chile, wanda ita ta lashe gasar a garin Santiago wancan karo da aka buga. An tashi wasan ne babu ci tsakanin Kasar Chile da ta Argentinar su Messi, wanda ya kai har an kara lokaci, amma dai ina, ba a samu wanda ya ga zare ba. Wannan ya kai aka buga finariti (watau bugun daga kai-sai mai tsaron gida), Wajen finaritin ne dan wasa Lionel Messi ya zubar da na sa, sannan kuma Lucas Biglia shi ma ya barar da na sa daga baya, wannan dai yaba Kasar Chile nasara.

Bayan an tashi wasan ne, Messi (cikin bacin rai) yake cewa: “Ni da buga ma Kasa kuma an gama, na rasa wasannin karshe (na Finals) har sau 4, ban da rabo. Na yanke shawara, ina tunanin ta kare!” Lionel Messi ya kara da cewa: “Ina mai matukar takaici ace hakan ya kara faruwa, na zubar da dukan finariti na, finaritin nan na da matukar tasiri.”

Shi kuwa Ronaldo cewa yayi: “Zabi ne na Messi, dole mu yarda da wannan. Amma ba mu ji dadin hakan ba, muna fata ya sauya shawara.” Shi kan sa Ronaldo sai da ya rasa kofin duniya watau WORLD CUP da kuma gasar Nahiyar Amurka na COPA AMERICA kafin daga baya ya zo ya dauki kofunan da Kasar Brazil. Tuni dai Shugaban Kasar Argentina, Mauricio Macri yace ya tattauna da dan wasa Lionel Messi dangane da ajiye kwallon da yayi.

KU KARANTA: ZLATAN IBRAHIMOVIC ZAI KAMMALA  KOMAWA MANCHESTER

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel