Neymar zai yi zaman sa a Barcelona har 2021

Neymar zai yi zaman sa a Barcelona har 2021

– Neymar ya sanya hannu a wani sabon kwantiragi na shekaru 5.

– Farashin sa ya tashi zuwa fam  £167m, zai kai har fam £209m nan da Shekaru 3.

– Dan wasa Neymar yaci kwallaye 55 cikin wasanni 93 na La-liga a Barcelona.

– Neymar dai ya zo Barcelona ne daga Santos na Brazil a kan farashi fam miliyan 48.6 a 2013.

Tauraron Kasar Brazil, Neymar zai cigaba da wasa a Kulob din Barcelona badi, bayan ya kara tafka hannu a wani sabon kwantiragi, Kungiyar Barcelona ta bada wannan sanarwar. A jiya dadaddare, dan wasan mai shekaru 24 da haihuwa ya bayyana cewa zai yi zaman sa a Barcelona. Wannan dai ya sa farashin Neymar din ya tashi a kasuwa; duk mai son dan wasan sai ya biya fam miliyan £167, nan da shekaru 3 masu zuwa kuma sai ya kai wajen fam miliyan £209.

KU KARANTA: ZLATAN IBRAHIMOVIC ZAI KOMA MANCHESTER UNITED 

Neymar zai yi zaman sa a Barcelona har 2021

 

 

 

 

 

Shugaban Kungiyar Barcelona ta Kasar Spain, Josep Bartomeu a baya, ya tabbatar da cewa ana tattaunawa da Neymar Jr. Dan wasan ya sanar ta shafin sa na twitter cewa, yana matukar murna, zai cigaba da bugawa Barcelona, a jiya da dare. Wannan dai ya kawo karshen cece-kucen da ake tayi game da ‘dan wasan, a baya Kungiyar PSG da Manchester United suna neman sa.

KU KARANTA: ZLATAN IBRAHIMOVIC ZAI KOMA MANCHESTER UNITED DA GARA LEDA.

Dan wasa Neymar yaci kwallaye 55 cikin wasanni 93 a La-liga ya zuwan sa Barcelona daga Kulob din Santos na Brazil a kan farashi fam miliyan 48.6 a Shekarar 2013. Haka kuma ya ci ma Kasar sa kwallaye 46 cikin wasanni 70 din da ya buga. Har way au, Neymar dai ya ci kofin La-liga da Copa del rey sau 2, da kuma kofin UEFA Champions Leauge sau 1 a shekarar 2014/15.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel