Buhari ya kira ma'aikatan sansanin yan hijira
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kira ma’aikatan da ke kula da ‘Yan gudun Hijira (IDP) a Jihar Borno game da yadda mutanen ke tagayyara suna mutuwa. Da alamu ma’aikatan da ke kula da wadanda rikicin Boko Haram ya auka da su, suna cikin babbar matsala bayan da Shugaban Kasar ya kira su, Shugaban Kasar na neman bayanin abin da ke faruwa a sansanen, Shugaban yana bukatar ayi masa bayani yadda mutanen suka shiga wani hali. Muhammadu Buhari ya gana da Mai’aikatan bada taimakon agaji na gaggawa na Jiha da ma Tarayyar Kasar a fadar Gwamnati, Aso Rock, a ranar Litinin.
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa ran Shugaban Kasar yayi matukar baci game da tabarbarewar abubuwa a matsugunin ‘Yan gudun Hijiran (IDP) ganin irin makudan Kudin da ake tura masu ta hanyar gwamnatocin jihohi da tarayya da kuma sauran kafafe. Shugaban Kasar ya gana da ma’aikatan na SEMA da NEMA ne bayan wata kungiya mai suna Doctors Without Borders (MSF) ta fitar da hotunan yadda mutane ke tagayyara a sansanun. Kungiyar dai ta gano kaburbura kusan 1,233 wanda fiye da 480 na kananan yara ne, a kusa da sansanen ‘yan gudun hijira. Binciken Kungiyar Doctors Without Borders (MSF) din ya nuna cewa fiye da ‘yan gudun hijira 24,000 suna cikin wanni mummunan yanayi, haka dai akalla mutane 6 ke mutuwa kullum, musamman kananan yara.
Mako 2 da suka wuce Gwamnan Jihar, Kashim Shettima ya ziyarci wani sansanen ‘yan gudun hijiran da ke Garin Bama bayan ya samu labari cewa wadanda aka kubutar daga Boko Haram suna karasa mutuwa ne a cikin sansanen. Nan-take dai Gwamnan ya bada umarnin a wuce da yara 61 masu fama da matsalar rashin isasshen abinci zuwa Asibiti a Maiduguri. Ko a baya, kungiyar nan ta Doctors Without Borders (MSF) ta dauke mutane 1,192 domin sama masu maganguna.
Gwamnan Jihar Bornon Kashim Shettima ya bayyana cewa yana da niyyar maida kowa gidan sa zuwa Disamban 2016.
Asali: Legit.ng