Tirkshi : Namiji da ciki

Tirkshi : Namiji da ciki

-An samu wani namiji da ciki, an yi tsamannin abin wasa ne, ashe da gaske ne. Gashi an samu wani kuma yanzu kuma yana gab da haihuwa.

A shekaru 8 da suka gabata yanzu, shekarar 2008 , an samu wata gagarumin labarin cewa wani namijin da aka canza al'auran sa zuwa farji yayi ciki. sunan shi Thomas beatie. Kai har shirin telebijin din Oprah ya fito.

Tirkshi : Namiji da ciki

Gashi an samu wani mai cikin kuma namiji a kasar china. Sunan shi zhang chang. Kamar yadda kuga gani a hoton , gashin nan da ciki a kumbure kaman mai jirar nakuda. Yanada shekaru 33. Amma ya samu ciki ne tun shekarar 2004 kuma sai wannan shekaran 2016 aka samu cire masa. Matsala shine wannan cuta ne a cikinsa ba ciki ba saboda kullun kara girma ya ke yi.

KU KARANTA: Kasashe 5 da ka iya ficewa daga Kungiyar EU.

Liktoci sun ki daukar kasadan yi masa aiki zai iya mutuwa. Dangin sa sun dare suna tara kudi domin yi masa aiki saboda tsadar sa. Daga baya da akayi aikin, sai aka dau tsawon awa 6 anayi. Daga karshe, an ci nasara kuma ya na nan da sauki.

Tumbin ta hana shi samun budurwa, ta hana shi aure. Amma yanzu yana cikin farin ciki da jin dadi, kuma muna mai kyakkyawan zati zuwa har ya karashe rayuwan shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng