Yan sanda sun yi dirar Mikiya a wani masallaci

Yan sanda sun yi dirar Mikiya a wani masallaci

-‘Yan sanda a jihar Kogi sun kai sumame kan wani masallaci, sun kame mutane da yawa

-Ana zargin masu satar da mutane da fakewa a masallacin

-‘Yan sanda sun yi amfani da bayanan  sirri wajen kai sumamen da kuma kamen wadanda ake zargi

Kimanin mutane 33 ne wadanda ake zargin da satar mutane ‘yan sanda suka kai musu a sumame a wani masallaci a Odu-Ape da ke kan hanyar zuwa Kabba a jihar Kogi.

Yan sanda sun yi dirar Mikiya a wani masallaci

A cewar jaridar This Day, wadanda aka kame ana zargin cewa masu satar mutane ne, kuma suna fakewa ne a wurin ibadar. ‘Yan sanda sun yi musu dirar mikiya ne a lokacin da suke tsaka da yin wani taro na musamman. Rahoton ya ci gaba da cewa masu satar mutanen sun fito ne daga yankin hanyar zuwa Obajana, kuma wani dan sandan farin kaya ne wanda ya yi shigar burtu a cikinsu, ya tseguntawa ‘yan sanda taron.

KU KARANTA: Musa yaron da kishiya ta sabauta ya murmure

Mai ba gwamnan jihar Kogi shawara na musamman a harkar tsaro, Commodore Jerry Omodara mai ritaya ne ya tabbatarwa da manema labarai faruwar lamarin a ranar Laraba 22 ga watan Yuni. Ya kuma jaddada cewa gwamantin jihar ta shirya tsaf wajen ganin kawo karshen masu aikata miyagun laifuka a jihar.

A wani labarin kuma, wasu wadanda aka sace a yankin an sake su bayan sun biya Naira miliyan 1 da 500,000 kudin fansa. A hirarsa da 'yan jaridu, daya daga cikinsu ya ce an sace su ne a kusa da wani wurin biciken 'yan sanda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng