Wani dan Majalisa yayi kaca-kaca da ‘Fitinanne’ Fayose

Wani dan Majalisa yayi kaca-kaca da ‘Fitinanne’ Fayose

- Wani dan Majalisa yayi kaca-kaca da ‘Fitinanne’ Fayose

– Wani dan Majalisan Najeriya, Segun Olulade yayi kira ga jam’iyyar PDP da ta gaggauta kiran Gwamna Ayo Fayose ya dawo zuwa cikin hankalin sa.

 – Dan Majalisar yace ya kamata Gwamna Fayose yayi hankali, ganin cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bai taba maida masa martani ba duk surutan banzan da yake yi.

 – Yace kokarin ya tsoma sunan mai dakin Shugaba Buharin cikin badakalar ‘Halliburton’ shirme ne, a maimakon ya tsaya yayi aikin sa na Gwamna da ya gaza.

 - Dan majalisar dokokin Jihar Legas mai wakiltar mazabar Epe, Segun Olulade, ya bayyana Gwamnan Jihar Ekiti a matsayin wani mai nema ya zama ‘fitinanne’

Wani dan Majalisa yayi kaca-kaca da ‘Fitinanne’ Fayose

Ya kira jam’iyyar PDP da ta maido da shi cikin hayyacin Sa. A wani bayani da ya zo ma Legit.ng, Olulade yake cewa yana mamakin yadda Fayose ya zama ba sa da aikin yi sai zagin Shugaba Muhammadu Buhari, yanzu har abin ya kai ga mai dakin Sa, Hajiya Aisha Buhari. Dan majalisar wanda shine Shugaban kwamitin lafiya a majalisar dokokin Jihar Legas yace tun da Fayose yake zagin Shugaba Buhari, har yau ko sau daya, Shugaba Buharin bai taba kula sa ba. Inda yana da hankali da yanzu duk ya gaji ya daina wannan haukan da yake yi, amma A’a, sai ya koma kan matar Sa, cewar Olulade.

Olulade yake bayyana yunkurin jefa sunan matar Shugaban Kasar cikin badakalar Halliburton a matsayin wani aikin banza, da kuma kokarin kauda kan mutane daga matsololin da ya jefa Jihar da yake mulki ciki. Mutanen Jihar Sa na yajin aiki, amma Gwamnan na nan yana zagin matar Shugaban Kasa, maimakon ganin yadda zai kawo karshen matsalar.

“Idan har Fayose na da gaskiya, bai amfana da kudin makamai da Sambo Dasuki ya rabar ba, ya je ya fuskanci shari’a, ya daina karyar yana da wata garkuwa a doka,. Yaje ya wanke kan Sa, ya daina yaudarar ‘Yan Najeriya, Ya je ya nuna karya ne, bai ci kudin Dasuki ba. Shikenan.” Inji Segun Olulade.

Da wannan nake cewa jami’yyar sa (Fayose) ta PDP ta kira sa, ya dawo cikin hankalin Sa, ya daina zagin Shugaban Kasa Buhari. Olulade ya karasa maganar Sa.

 

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng