Fayose mahaukacin kare ne- Aisha Buhari

Fayose mahaukacin kare ne- Aisha Buhari

-Matar shugaban kasa Muhammad buhari, Hajia Aisha Muhammad buhari ta ce gwamnan jihar ekiti, Ayodele fayose , Mahaukacin kare ne.

-Gwamna Ayodele fayose ya zarge ta ne a jiya da kashi a gindi na cin hanci da dan majakisan wakilan kasar amurka, William Jefferson.

Fayose mahaukacin kare ne- Aisha Buhari

Abun dai da ban tsoro, da ban mamaki, matar shugaban kasa Muhammad Buhari wato Hajia Aisha Muhammad Buhari ta kira wannan gwamnan adawa nan dai Ayodele Fayose na jihar ekiti, Mahaukacin kare.

Hajia Aisha Buhari ta mayar da wannan martani ne cikin fushi saboda zargin da shi Ayodele Fayose ya mata a idon duniya, na cewa ta taba aikata cin hanci da dan majalisan wakilan kasar amurka, William Jefferson.  Shi Jefferson dai an gurfanar da shi a amurka a shekarar 2009. Matar shugaban kasan ta fadi wannan ne a wani sako da ta rubuta a shafin sadarwan ta na twitter a jiya 21 ga watan yuni .

Tace:

“Gaskiya wannan cin fuskan ya isa fayose, Mahaukacin karen da bai daure. Naki in yi shiru wannan karon.  Ka sani cewa, idan buhari na da shekara 73, ni Aisha shekaru na 45 ne kacal, ina da isasshen karfin fafatawa da kai”.

KU KARANTA: Muna rokon Fayose ya ceci rayukan mutane Jihar Ekiti- APC

Haka zakika, manyan lauyoyin najeriya da yan yakin neman hakkin bil adama da dama na ta tifa albarkacin bakin su akan daskarar da asusun bankin Gwamnan jihar Ekiti Ayodele foyose da hukumar hana al mundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zama kasa watau EFCC tayi a ranar litinin 20 ga watan yuni 2016.

Gwamna Ayodele Fayose dai na kukan cewan hukumar hana cin hancin da rashawan sun take hakkin sa. Yace  a matsayin sa gwamna mai ci, kundin tsarin mulkin kasa ts bashi kariya to kowani fanni . amma hukumar EFFC ta ce kudin tsarin mulkin kasa ta ba ta karfin bincike da kuma daskarar da asusun koma waye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng