Buhari ya sake jerin sunayen jakadai
-Shugaban kasa Muhammdu Buhari ya bayyana jerin sunayen jakadai da aka kebe
-Wannan yana kunshe acikin wata wasika da aka aika zuwa ga majalisar dattijai
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake jerin sunayan wadanda aka kebe dan matsayin jakadanci a rana Alamis, 9 ga watan Yuni. Wannan yana kunshe ne cikin wata wasika da aka aika zuwa ga shugaban dattijai, Bukola Saraki.
KU KARANTA: Osinbanjo da Jonathan sun nuna jimamin mutuwar Keshi
An bayyana hakan ne bayan Saraki ya karanta jerin sunayen jakadai 47 da ke kasa a majalisar dattijan. wadanda aka kebe mutane ne da zasu kula da manufar Najeriya a kasar waje.
Wadanda aka kebe sun hada da, Obinna Chukwuemeka, Salisu Umoru, Iyang Udoh Iyang, Okeke Vivian Nwanaku, Niman Munir, Edem Jane Ada, Muhammed Hassan Hassan, Martin Young Cobham, Janet Molegbo Olisah, Itegbuoye Sunday, Olatunde Adesesan, Lilian Ijekwu Onu, Manaja Tulahi Isa, Ngozi Ukeje, Bello Kazaure Huseini, Inoc Pierre Ducci, Garba Baba, Usman Bakori Aliyu, Umar Zainab Salisu, Momoh Seyidou Umieza, Kadri Ayinla, Balogun, Hakeem, Nosa Ahmed, Ibrahim Isa and Bankole Adegboyega Adeoye.
Sauran sun hada da, Ibidapo Obe Oluwasegun, Ogundayo Sakirat, Eric A. Belgam, Ateru Aliru, Ramata Bulima, Musa Rahman, Kabiru Bala, Damu Shuaibu, D. A Agiv, TK Gonglong, Ibrahim Hamza, KC Nwachukwu, Q.R Lolu, E.K Oguntuwase, A.I Paragauda, L.A Gasharga, Olufemi Abikoye, Abubakar Ibrahim, Rabiu Kauru, Odeka Janet Biong and Adekunbi Habeebat.
Asali: Legit.ng