Tsagerun Nija Delta sun sha alwashin kashe Buhari

Tsagerun Nija Delta sun sha alwashin kashe Buhari

Kungiyar tsirarun Niger Delta Wanda aka fi sani da Niger Delta Avengers(NDA) sun sha alwashin hallaka shugaba Buhari.

Tsagerun Nija Delta sun sha alwashin kashe Buhari
Wasu Tsagerun Niger Delta

Daya daga cikin en kungiyan Wanda aka ji muryar sa ta wayar tarho wanda aka dauka akan gidan radio ta Biafra tace shugaba Buhari ya rubuta wahayin sa ta karshe a duniya idan ya shigo kasar kudu mask kudu ta Najeriya.

KU KARANTA: Makiyaya sun kai hari a Jihar Benue, sun kashe 18

Mai maganan ya kuma jaddada cewa duk Wanda ya tallafa wa shugaban kasa Buhari zasu hallakashi.

Wannan firar wayar tarho Wanda aka aika wa IBTimes ta kasar Ingila da kafar radio Biafra yace basu lamunce wa shugaba Buhari yashigo kasar ta Niger Delta ba Wanda take da arzikin albarkatun mai da gas.

Shugaba Buhari sai ya shirya ziyartar kudu maso gabas dakuma kudu maso kudu ta Najeriya Don tuntubar shuwagabanni da dattawan yankunan saboda ayyukan ta'addan tsirarun Niger Delta da masu yunkurin Neman kasar Biafra, sanna kuma ya kaddamar da sharar gyara muhallin yankin daga ranar alhamis 2 ga watan June.

Tsirarun en bindigar Niger Delta Avengers sun cigaba da fasa bututun mai da gas run hawar shugaba Buhari karagar mulkin Najeriya Wanda hakan ya matukar gurgunta adadin mai da gas da Najeriya take fitarwa!

Kungiyar sun yi tur da kashe en yunkurin Biafra da sojojin Najeriya tayi a kwanakin bayannan kuma tayi kira a cigaba da yiwa Nnamdi Kalu shugaban en Biafra ta IPOB Wanda yake tsare a hannun jami'an tsaro visa zargin yunkurin yiwa kasa zagon kasa.

Brigadier General Rabe Abubakar yayi watsi da yunkurin en tada zaune tsayen inda ya jaddada cewa shugaban kasa Buhari yana da ikon Shiga kowace yanki ta Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng