Shugaban kasa Buhari ya kori shugaban Immigration

Shugaban kasa Buhari ya kori shugaban Immigration

- Shugaban kasa Muhmmadu Buhari ya umurci shugaban hukumar Immigration, Martin Abeshi da yayi murabus

- Wannan yazo ne saboda yadda shugaban yake taka dokar aiki

- Jami'an hukumar sunyi murna da korar shi da akayi

Shugaban kasa Buhari ya kori shugaban Immigration
Martin Abeshi wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kora a jiya sakamakon zargin rashawa da ake yi mashi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kori shugaban hukumar Immigration, Martin Abeshi daga bakin aikin shi a jiya Talata 17 ga watan Mayu na 2016.

Jaridar Vanguard ta bayyana cewa ana tsammanin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kore shine saboda yadda yayi da daukar aikin ma'aikata a hukumar.

Jami'an hukumar sunyi murnar sosai inda suka bayyana cewa dama suna zargin shi da aikata rashawa da karbar kudade daga hannun ma'aikata domin ya tura su aiki kasar waje.

A kwanakin baya, wasu jami'an hukumar sun aika da korafi zuwa shugaban kasa Muhammadu Buhari inda suka nemi shugaban kasa daya binciki shugaban hukumar akan wasu zarge-zarge na rashawa da ake yima shugaban hukumar ta immigration din.

An nada Abeshi ne a watan Satumba na 2015 inda a lokacin bai wuce watanni 3 ba ya tafi hutun barin aiki. David Parradang ne ya sauka Abeshi ya hau, bayan da aka zargi Parradang da hannun cikin iftila'in daya auku a lokacin daukan ma'aikata a hukumar a 2015.

Wannan ne ya sanya da yawa cikin mataimakan shugaban hukumar basu jin dadin zaman shi Abeshi a hukumar domin wasu na ganin ya tare masu wuri domin yaki yin murabus.

A wani labarin kuma, a yau a Najeriya an tashi da yajin aiki bayan da gwamnatin najeriya ta kai kungiyar kwadago kotu, ina kotu ta hana su yajin aikin. Amma yan kungiyar sunyi kunnen uwar shegu da umurnin kotun inda suka tafi yajin aikin a yau.

Wasu daga cikin kungiyoyin da suke karkashin uwar kungiyoyin, watau NLC da TUC sun bayyana cewa su baza su shiga cikin yajin aikin ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng