Da Duminsa: Babban Sarki a Arewa, Dr Shekarau Agyo, ya riga mu gidan gaskiya

Da Duminsa: Babban Sarki a Arewa, Dr Shekarau Agyo, ya riga mu gidan gaskiya

Jihar Taraba - Aku Uka na kasar Wukari a jihar Taraba, Dr Shekarau Agyo ya riga mu gidan gaskiya.

A ruwaiyar Daily Trust, basaraken ya rasu ne a ranar Asabar a fadarsa da e Wukari bayan ya dade yana fama da rashin lafiya.

Da Duminsa: Babban Sarki a Arewa, Dr Shekarau Agyo, ya riga mu gidan gaskiya
Aku-Uka na kasar Wukari, Dr Shekarau Agyo, ya rasu. Hoto: Daily Trust
Source: Facebook

Marigayi Aku-Uka, sarki ne mai sandan daraja ta farko kuma shugaban majalisar sarakunan jihar Taraba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An nada shi sarauta a matsayin Aku-Uka na Wukari na 27 a watan Agustan 1976, an kuma haife shi a shekarar 1973.

Majiyoyi na kusa da gwamnatin jihar Taraba sun shaidawa Daily Trust cewa gwamnan jihar Taraba ne kadai zai iya sanar da rasuwar sarkin a hukumance bayan an yi wasu abubuwa na kabilar jukun.

Ku saurari karin bayani ...

Source: Legit Nigeria

Online view pixel