Anyi jana'izar mutum 35 cikin 38 da aka kashe a harin Kaduna
- An bizne mutanen da yan bindiga suka kaiwa harin bazata a jihar Kaduna
- Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufa'i ya yi Alla-wadai da harin
- Gwamnatin jihar tace mutum 34 aka kashe amma gawawwaki 38 aka gano
An yi jana'izar mutum 35 cikin mutane 38 da aka kashe a kudancin Kaduna ranar Lahadi, 26 ga watan Satumba.
An jinkirta jana'izar sauran mutum ukun ne saboda gawawwakinsu sun kone kurmus da an gaza ganesu, rahoton Sahar Reporters.
An yi jana'izarsu ne a Madamai, karamar hukumar Kaura ta jihar.
Gwamnatin Kaduna ta tabbatar barkewar rikici a jihar
Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar labarin kisan mutane talatin da hudu da yan bindiga sukayi a karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna ranar Lahadi.
Mun kawo muku cewa wasu batagari sun kona gidaje a kauyukan Madamai da Abun dake karamar hukumar Kaura a jihar Kaduna.
Kwamishanan tsaro da lamuran cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya saki jawabi ranar Litinin, 27 ga Satumba, 2021.
A cewarsa, kawo yanzu mutum 34 aka tabbatar da an kashe yayinda Sojoji suka kashe wutar daka cinnawa gidaje.
Gwamnan Kaduna ya yi alhinin abinda ya faru, yayi alkawarin biyan kudin jinyan wadanda ke asibiti
Samuel Aruwan ya bayyana cewa gwamna Nasir El-Rufa'i na jihar ya yi Alla-wadai da wannan abu.
Gwamnan ya ce gwamnatin jihar za ta dauki nauyin jinyar wadanda suka jikkata kuma suka jinya a asibiti yanzu.
Asali: Legit.ng