Da duminsa: Duk da yayi sata, Kotu ta haramtawa hukumar EFCC sake gurfanar da Sanata Orji Kalu

Da duminsa: Duk da yayi sata, Kotu ta haramtawa hukumar EFCC sake gurfanar da Sanata Orji Kalu

Babbar kotun tarayya dake zaune a Abuja ranar Laraba, ta haramtawa gwamnatin tarayya sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, kan laifin almundahanar N7.1billion.

A hukuncin da Alkali Inyang Ekwo ya yanke, ya bayyana cewa kotun koli bata bayyana karara a hukuncin da ta yanke ranar 8 ga Mayu, 2020 cewa a sake gurfanar da Kalu da kamfaninsa, Slok Nigeria Limited ba.

Alkali Ekwo ya bayyana cewa wanda kotun koli ta bada umurnin sake gurfanarwa shine tsohon diraktan kudi na gwamnan jihar Abia, Jones Udeogu.

Saboda haka, kotun ta amince da bukatar Kalu inda ya kalubalanci shirin sake gurfanar da shi da EFCC ke yi.

Da duminsa: Duk da yayi sata, Kotu ta haramtawa hukumar EFCC sake gurfanar da Sanata Orji Kalu
Da duminsa: Duk da yayi sata, Kotu ta haramtawa hukumar EFCC sake gurfanar da Sanata Orji Kalu
Source: UGC

Read also

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

Source: Legit.ng

Online view pixel