Zamu samawa yan Najeriya milyan 20 wutan lantarki nan da 2030, Buhari
1 - tsawon mintuna
- Shugaba Buhari ya gana da shugabannin kasashe a Amurka kuma ya bayyana musu aniyarsa
- Shugaban kasan ya bayyana sabuwar hanyar samawa yan Najeriya wuta nan da 2030
- Najeriya na fama da matsalar wutar lantarki musamman masana'antu
New York, Amurka - Shugaba Muhammadu Buhari yace gwamnatin Najeriya na shirye-shirye samar da isasshen wutan lantarki ga yan Najeriya nan da shekarar 2030.
Mai magana da yawun Shugaban kasa, Femi Adesina, a jawabin da ya saki da yammacin Juma'a ya ce Buhari yayi wannan bayani ne a tattaunawarsa a taron majalisar dinkin duniya dake gudana a Amurka.
A cewarsa, Najeriya zata samar sabon hanyar samar da wuta daga hasken rama domn rage dogaro kan iskar Gas.
Buhari yace:
"Yunkurin da Najeriya ke yi wajen inganta wutan lantarki ya bayyana a sabon aikin samar da wuta a gidaje milyan biyar da mutane milyan ashirin ta hanyar amfani da hasken rana."
"Wannan shine mataki na farko wajen rage matsalar wuta nan da 2030."
Shugaban Najeriyan ya yi kira ga kasashen da suka cigaba su taimakawa Najeriya da kudi wajen cimman wannan manufa.
Asali: Legit.ng