An bude gidan cin kaji da abinci da ya shahara a duniya, KFC a jihar Kano
Daga cikin yunkurin cigaba da dabbaka koyarwan Kanal Sanders, Shahrarren Kamfanin KFC Nigeria ya shigo birnin Kano domin jin dadin al'ummar kasar Dabo.
An fara bude shagon KFC Nigeriya na farko ne a 2009, tun lokacin kamfanin ke cigaba da jan ra'ayin jama'a saboda irin kayan dadin rayuwa da take sayarwa a sassan Najeriya daban-daban.
Ko shakka babu, KFC ya samu karbuwa a fadin Najeriya da wannan sabon shago da ta bude a birnin kasuwancin Arewa, jihar Kano.
Wannan na nuni da cewa kowani dan Najeriya ya cancanci jin dadin kazar Kanal.
Yanzu, al'ummar Kano zasu iya jin dadin dukkan kayan dadin da KFC ke sayarwa kulli yaumin cikin sauki.
A sakon da Legit ta samu, sabon gidan da kamfanin ya bude ta Kano na sayar da Kaji, Yamilicious mai yaji , sabon tukunyar Shinkafa, da kuma sabbin kayyakin dadi.
Sakon ya kara da cewa za'a cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
1. Za'a rika bude shagon ne daga karfe 9 an safe zuwa 10 na dare
2. Za ka iya oda ta Jumia Food ko kuma a garzaya Ado Bayero Mall ka saya da kan ka/ki
2. Ana shirin bude sabbin rassa a fadin jihar
Kamfanin ya jaddada cewa kiwon lafiyar al'umma wajen girki da cin abinci abune wanda ta dauka da muhimmanci kuma ba zata gushe wajen tabbatar da hakan ba a dukkan shagunansa.
Hakazalika, za'a tabbatar da ma'aikatan wajen tare masu zuwa diban girki su bi dokokin sanya takunkumin rufe baki da kuma wanke hannu.
Asali: Legit.ng