Waiwaye: Ina da jinin Fulani da Musulunci, Kakata Bafulatana ce, Kakana Musulmi ne: Fani-Kayode

Waiwaye: Ina da jinin Fulani da Musulunci, Kakata Bafulatana ce, Kakana Musulmi ne: Fani-Kayode

  • Ana cigaba da Waiwaye kan abubuwan da Fani-Kayode ya fada a baya
  • Daya daga cikinsu shine cewa yana da jinin Fulani daga bangaren iyayen mahaifiyarsa
  • Hakazalika yace mahaifin Kakansa babban Malamin addinin Musulunci ne

Cigaba da waiwaye kan abubuwan da tsohon ministan Sufurin jirgin sama, Femi Fani-Kayode yayi, an gano lokacin da yace mahaifiyar Kakarsa Fulani ce daga jihar Sokoto.

Premium Times da TheCable sun ruwaito Fani-Kayode da dewa Kakansa babban malamin addinin Musulunci ne mai suna Sheikh Nurudeen Sa'id.

Fani Kayode ya kara da cewa Sheikh Sa'id dan asalin garin Ilesha a jihar Osun ne kuma ma'aikacin gwamnati ne mazaunin Legas.

Yace:

"Mahaifinsa, wanda shine mahaifin kakata, Bayarabe ne daga Ilesha. Amma maihaifiyarsa, wacce itace mahaifiyar kakata, Fulani ce daga Sokoto."
"Kakana kuwa, Sheik Nurudeen Sa'id, wanda rabinsa Fulani ne kuma rabi Bayarabe, ya auri Kakata, Alhaja Abeke Sa’ id (nee Williams), "

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen dan majalisar arewa ya bayyana dalilin da ya sa APC ke zawarcin Jonathan, ya yi magana akan kudirin Tinubu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Yar Legas ce kuma diyar Alhaji Isa Williams wanda babban jagoran Musulmai ne a Legas kuma babban dan kasuwa mafi arziki a Legas lokacin."

Waiwaye: Ina da jinin Fulani da Musulunci, Kakata Bafulatana ce, Kakana Musulmi ne: Fani-Kayode
Waiwaye: Ina da jinin Fulani da Musulunci, Kakata Bafulatana ce, Kakana Musulmi ne: Fani-Kayode
Asali: UGC

Ina gidan Farfesa Pantami jiya har cikin dare, mun debi girki kuma mun tattauna: Femi Fani-Kayode

Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya yi takakkiya zuwa gidan Ministan Sadarwa da tattalin arziki na zamani, Farfesa Isa Ali Pantami dake birnin tarayya Abuja.

Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Facebook, Fani-Kayode yace Farfesa Pantami ne ya gayyacesa kuma ya amsa.

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya yi wa Femi Fani-Kayode rakiya yayin ziyarar.

Wannan ya faru ne kwana daya bayan Fani-Kayode sauya sheka jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel