Da duminsa: Ba zamu dakatad da yajin aiki ba, Likitoci sun garzaya kotun daukaka kara

Da duminsa: Ba zamu dakatad da yajin aiki ba, Likitoci sun garzaya kotun daukaka kara

  • Likitoci sun yi martani kan hukuncin kotun m'aikata NIC
  • Likitocin sun fara yajin aiki ne ranar 1 ga Agusta bisa rashin biyansu albashi da kuma sauran wasu dalilai
  • Alkalin kotun yace mutane zasu cigaba da mutuwa idan Likitoci basu koma aiki ba

Abuja - Shugabannin kungiyar Likitoci masu neman kwarewa a Najeriya NARD sun yi Alla-wadai da hukuncin kotun ma'aikatan Najeriya da ta umurci mambobinta su koma bakin aiki.

A takardar da Shugaban kungiyar, Dr Uyilawa Okhuaihesuyi, da Sakataren kungiya Dr Jerry Isogun, suka saki ranar Juma'a. sun bayyana cewa sun fara daukaka kara.

Jawabin yace:

"Kamar yadda muka sani, musamman wadanda ke kotu yau, kotu yau... Bamu gamsu da hukuncin kotu ba."
"Bayan tattaunawa da Lauyoyinmu, mun umurcesu su daukaka kara kuma su nemi a dakatad da aiwatar da umurnin kotun."

Kara karanta wannan

Da dumi: Kotu ta umurci Likitoci su janye daga yajin aiki

Shin zasu koma aiki ne?

Maimakon umurtan mambobinta su koma bakin aiki, kungiyar Likitocin tace lauyoyinta su koma kotu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika ta umurci mambobin su kwantar da hankulansu.

Suka ce:

"Muna kan bakanmu na cigaba da kare hakkinku. Mun yi imanin zamu samu nasara."

Da duminsa: Ba zamu dakatad da yajin aiki ba, Likitoci sun garzaya kotun daukaka kara
Da duminsa: Ba zamu dakatad da yajin aiki ba, Likitoci sun garzaya kotun daukaka kara

Kotu ta umurci Likitoci su janye daga yajin aiki

Kotun ma'aikatan Najeriya ta umurci Likitocin kungiyar Likitoci masu neman kwarewa (NARD) su dakatar da yajin aikin da sukeyi ba tare da bata wani lokaci ba.

Likitocin sun fara yajin aiki ne ranar 1 ga Agusta bisa rashin biyansu albashi da kuma sauran wasu dalilai.

Alkalin kotun, Bashir Alkali, yace yayi imanin cewa idan kotu bata sa baki yanzu ba, babu adadin kudin da zai iya dawo da rayukan yan Najeriya da za'a rasa idan Likitoci suka cigaba da yakin aiki.

Saboda haka ya ya amince da bukatar gwamnati kuma na basu gaskiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel