Da Duminsa: Kotu Ta Umurci Gwamnatin Buhari Ta Biya Sunday Igboho Naira Biliyan 20

Da Duminsa: Kotu Ta Umurci Gwamnatin Buhari Ta Biya Sunday Igboho Naira Biliyan 20

  • Wata Babban kotu a jihar Oyo ta umurci gwamnatin tarayya ta biya Sunday Igboho diyyar Naira Biliyan 20
  • Sunday Igboho ya shigar da kara a kotun ne don neman a bi masa hakkinsa kan samamen da SSS ta kai gidansa
  • Kotun ta ce samamen da SSS ta kai gidan dan gwagwarmayar keta hakkin bil adama ne kuma ta tabbatar yana da ikon yawo da walwala

Oyo - Wata babban kotun jihar Oyo, a ranar Juma'a ta sanyayawa mai rajin kare hakkin Yarbawa, Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho rai, inda ta umurci gwamnatin Nigeria ta biya shi Naira Biliyan 20, SaharaReporters ta ruwaito.

Kotun ta kuma yi watsi da bukatar da Attoni Janar na Kasa, Abubakar Malami, SAN, ya shigar na kallubalantar hallarcinta na sauraron karar da aka shigar game da wasu hukumomin Nigeria.

Kara karanta wannan

Nnamdi Kanu ya maka kasar Kenya a kotu bisa laifin mika shi ga Najeriya

Da Duminsa: Kotu Ta Umurci Gwamnatin Buhari Ta Biya Sunday Igboho Naira Biliyan 20
Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Igboho ya nemi kotu ta umurci gwamnati ta biya shi diyyar N500bn

Ana sa ran kotun za ta yanke hukunci kan karar da Sunday Igboho ya shigar na neman gwamnatin Nigeria ta biya shi diyar Naira Biliyan 500 soboda keta masa hakkinsa na bil-adama da DSS ta yi.

Igboho, ta bakin lauyansa, Yomi Aliyu, ya shigar da kara yana kallubalantar samamen da DSS ta kai gidansa a ranar 1 ga watan Yuli.

Igboho, yana daya daga cikin mutanen da ake nema kotun ta ayyana cewa samamen haramtacce ne kuma keta hakkin biladama ne.

Wadanda Igboho ya yi kararsu sun hada da Atoni Janar kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, SAN, a matsayin na farko, SSS a matayin na biyu sai shugaban SSS na jihar Oyo a matsayin na uku.

Lauyan Malami ya ce kotun jiha bata da ikon sauraran kara da ta shafi SSS

Kara karanta wannan

Daga bisani, NAF ta dauka alhakin yi wa farar hula ruwan wuta a Yobe

Lauyan Malami, Abubakar Abdullahi ya shigar da kara yana kallubalantar da ikon babban kotun na jiha ta saurari kara kan abubuwan da suka danganci hukumar 'yan sandan farin kaya, DSS.

Tare da bada misalai da dama a shari'un da aka yi kotun daukaka kara da kotun koli kan hallarcin babban kotun jiha ta saurari irin wannan karar, Mai shari'a Ladiran Akintola ya ce samamen gidan wanda ya shigar da karar keta hakin bil adama kamar yadda kundin tsarin mulkin Nigeria ta 1999 ya tanada.

Ya ce:

"Kotu ba mai rabon garabasa bane don haka ba za ta iya amincewa ta umurci a biya mai shigar da kara Naira Biliyan 500 ba amma tana umurtar kada a kama ko cin mutuncin mai karar. Yana da ikon zirga-zirga kamar yadda ya ke a sashi na 35.1(a)(b) na kundin tsarin 1999."

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel