Gwamnoni 36 sun hada-kai, sun yi karar FG a Kotu, sun bukaci a dawo masu da kudin shekaru 5

Gwamnoni 36 sun hada-kai, sun yi karar FG a Kotu, sun bukaci a dawo masu da kudin shekaru 5

  • Gwamnatocin jihohi 36 sun kai gwamnatin tarayya a kotu kan harajin hatimin banki
  • Gwamnatin tarayya tana karbar haraji duk idan aka aika wa mutum kud i a akawun
  • Gwamnoni sun ce jihohi ya kamata su rika tattara harajin ba gwamnatin tarayyar ba

Premium Times ta rahoto cewa gwamnatocin jihohi sun kai karar gwamnatin tarayya bisa zargin kin ba su kudin da aka samu daga karbar harajin hatimi.

Gwamnoni 36 na kasar nan sun maka Ministan shari’a, Abubakar Malami a kotu, a matsayinsa na babban lauya kuma mai wakiltar gwamnatin tarayya.

Rahoton yace gwamnatocin sun roki kotu ta tursasa wa gwamnatin tarayya ta dawo masu da sama da Naira biliyan 176 da aka tara daga 2016 zuwa 2020.

A cewar gwamnatocin, jihohi ne suke da ikon karbar kudin hatimi ba jami'an gwamnatin tarayya ba.

Kara karanta wannan

Dokar VAT za ta talauta Jihohi 30, Gwamna Wike yace sai dai sama da kasa su hade

Har ila yau, kwanishinonin shari’ar a madadin gwamnoni, suna so kotu ta bayyana cewa ko Abubakar Malami SAN yana da hurumin taba kudin.

Me kwanishinonin shari’a suke nema a kotun koli?

An shigar da karar mai lamba SC/CV/690/2021 ne a kotun koli. Ana neman Alkalai su raba gardama kan abin da sashe na 4(2) na dokar harajin yace.

Gwamnoni
Buhari ya sa labule da Gwamnoni Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Kwamishinonin shari’a na jihohin Najeriya suna ikirari cewa a dokar kasa ba gwamnatin tarayya aka ba nauyin karbar kason harajin hatimi a cikin jihohi ba.

Shari’ar za ta raba gardamar ko gwamnatocin jihohi suna da hakkin 85% a cikin kason duk wani harajin hatimi da aka samu daga kudin da aka aika ta banki.

Hakan zai sa a hana duk wani jami’in gwamnatin tarayya karbar wannan haraji. Har zuwa yanzu, ba a sa ranar da za a soma sauraron wannan a kara a kotu ba.

Kara karanta wannan

Yan fashi sun taremu a hanya, sun kwace takardun kotu hannunmu, Lauyoyin DSS ga Alkali

Idan kwamishinonin sun dace a kotu, za a bar kowace jiha ta ci gashin kan-ta, ta karbi harajin da aka tara a jiharta daga kudin da suka shiga asusun bankuna.

Shari'ar VAT ta birkita lissafi

A makon nan aka ji cewa gwamnatocin Jihohi da-dama suna fuskantar kalubalen kudin tafiyar da Gwamnati saboda karar da gwamnatin Ribas ta kai FIRS.

Gwamnan Ribas, Nyesom Wike yace babu ja da baya kan wannan muradi. Gwamnan ya bukaci kamfanoni duk su daina biyan harajin VAT ga jami'an FIRS.

Asali: Legit.ng

Online view pixel