Kungiyar Kwallon Arsenal ta dauki dan Najeriya, Munir Sada, mai shekara 9 da haihuwa

Kungiyar Kwallon Arsenal ta dauki dan Najeriya, Munir Sada, mai shekara 9 da haihuwa

  • Dan Najeriya Munir Sada ya shiga kungiyar kwallon Arsenal a Ingila
  • Munir ne dan Arewacin Najeriya na farko da aka sani zai taka leda a Arsenal tun yana dan shekara 9
  • Yan Najeriya da dama sun tayashi murna yayinda wasu sukayi suka

Wani dan Najeriya mai shekara 9 da haihuwa, Munir Muhammad Sada, ya rattafa hannu kan kwantiragin taka leda da daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon duniya, Arsenal.

Arsenal na daya daga cikin manyan kungiyar kwallon dake kasar Ingila.

Legit ta tattaro cewa Munir Sada dan arewacin Najeriya zai rika taka leda a makarantar kungiyar yanzu yayinda ake sa ran wata rana zai haye.

Mun ji cewa Mahaifin Munir dan Zariya ne a jihar Kaduna yayinda mahaifiyarsa yar jihar Katsina ce.

Munir ne dan Arewacin Najeriya na farko da zai samu shiga kungiyar Arsenal tun yana yaro.

Kara karanta wannan

Buhari yace yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya yana da matukar wahala

Wasu yan Najeriya a baya irinsu Bukayo Saka sun samu irin wannan dama kuma yanzu sun zama manyan yan kwallo a duniya.

Kungiyar Kwallon Arsenal ta dauki dan Najeriya, Munir Sada, mai shekara 9 da haihuwa
Kungiyar Kwallon Arsenal ta dauki dan Najeriya, Munir Sada, mai shekara 9 da haihuwa Hoto: ONLY NIGERIA PLAYERS NEWS PAGE
Asali: Facebook

Yan Najeriya sun tofa albarkatun bakinsu kan nasarar Munir.

Yayinda wasu sukace wannan abun farin ciki ne da murna, wasu sunyi Alla-wadai inda suka ce ba zai samu tarbiyar addini ba.

Yahuza Adamu yace:

Gaskiya banyi murna ba tun kana yaro za'a rabaka da addininka.
Agaskiya bana farin ciki da kasance warka yaro mai qarimin shekaru kamata yayi ace yanzu haka kana makarantan da zaka koyi ibada ne ba a kaika harkan da za'a nemi kudi da kai ba.
Amma kowa danashi irin tunanin haka iyayen ka suka zaba maka.

Abubakar Dalhatu yace:

Wata kila Shine zai kawo sauyi a tarihin arsenal, in Sha Allah sanadiyar zuwansa a zamaninsa zai dauki kofin champions league da Sauran cup's dinda suka gagaresu dauka.

Kara karanta wannan

Yan kabilar Igbo ke rike da tattalin arzikin Najeriya, saboda me zasu bar kasar: Shugaba Buhari

Note: bansan Abunda zai faru gobe ba Kawai Nayi fatan hakane garesa tare Kuma nace Idan Allah ya yadda.

ابو خديجة الميسوى yace:

Kash! Inama ace amakarantar Haddar Qur'ani ya rattaba hannu,amma sai ya xabi Yahudanci,wanda kuma haramun ne.

Indallahi Tv yace:

Ruwa tasha yaro kayi kudi, kuda danginku kakarku tayanke saka, Allah yasa ta amfanar dakai da kasarka da addininka ameen.
Muna maka fatan alkhairi yaro

Abba Abbaty Musa yace:

Masha allah
Allah ya kara kwakwalwa ya kiyaye mana kai
Ka dawo gida na gaba ka kafa mana katafaren filin rainon yara masu shaawar kwallon kafa
Ka kuma daukaka Najeriya da sunanka

Asali: Legit.ng

Online view pixel