Naira ta yi kifewar da ba ta taba yi ba a tsawon shekaru 48, Dala $1 ta kai N550 a kasuwa
- Sai da mutane suka canji Dalar Amurka a kan N550 kafin a tashi kasuwa a jiya
- Rahotanni sun ce tun da aka kirkiri Naira a 1973, kudin bai taba yin kasa haka ba
- ‘Yan canji suna ganin Dala za ta iya haura N600 idan aka cigaba da tafiya haka
A ranar Alhamis, 9 ga watan Satumba, 2021, jaridar Punch ta kawo rahoto cewa Dalar Amurka ta doshi N543 a bankuna, abin da ba a taba ji a Najeriya ba.
Rahoton ya bayyana cewa ‘yan canji suna sayen Dala a kan N540, sannan sai su saida ta a N543. Ana kuma saida kudin Birtaniya, Dalar Pound a kan N740.
A yammacin jiya sai labari ya zo cewa Naira ta kara yin kasa a kasuwa. A ranar Alhamis sai da duk Dalar Amurka ta kai kusan N550 kafin a tashi kasuwa.
Naira ta karye da N20 a mako daya
Jaridar Daily Trust tace Dalar ta yi wani mugun tashi daga N530 a makon da ya gabata zuwa N550. Yawan neman Dalar ne ya jawo kudin yake ta kara tashi.
Bincike ya nuna cewa akwai yiwuwar Dalar Amurkar ta haura N550 ganin yadda ake neman ta ruwa-a-jallo a kasuwar canjin kudin ta Wapa BDC a Kano.
Shin Dala za ta sauko nan gaba?
Wani ‘dan kasuwar canji da ke garin na Kano, ya shaida wa manema labarai cewa kwanaki uku da suka wuce ana saida Dala ne a N520, jiya ta kai N550.
“Yawan bukata daga masu shigo da kaya suke yi ne ya jawo haka, a dalilin dokar da CBN ta kawo. Idan aka cigaba da haka, Dala za ta kai N600-N700.”
Masu canjin kudi ba su san ranar da abubuwa za su dawo daidai ba, suna ta kira ga gwamnan CBN ya dawo da ba ‘yan BDC Dala domin a samu sauki.
Tun da aka kirkiro kudin Naira a Najeria, ba a taba samun lokacin da Dala ta yi irin wannan tsada ba. Hakan ya sa jami’an EFCC suka shiga lamarin canjin kudi.
EFCC ta gargadi bankuna su daina bada Dala face ga wanda aka tabbata cewa zai bar kasar ne.
Dokar VAT za ta canza lissafi
Bincike ya nuna Gwamnoni 30 za su rasa inda za su sa kansu idan aka janye alhakin tattara harajin VAT daga hannun gwamnatin tarayya, aka ba jihohi.
Gwamnonin Legas da Ribas za su fi kowa amfana, Jihohi akalla 30 za su sha wuya domin baya ga karancin IGR. kudin da suke samu daga asusun FAAC zai ragu.
Asali: Legit.ng