Hotunan jami'ar yan sanda 'yar Katsina da ake ganin itace mafi kyau a Hukumar

Hotunan jami'ar yan sanda 'yar Katsina da ake ganin itace mafi kyau a Hukumar

  • Mutane sun tofa albarkacin bakinsu kan wata jami'ar yan sanda mai mukamin DSP yar jihar Katsina
  • Mutane da dama na cewa babu mace mai kyau irin DSP Fatima AbdulAziz a hukumar yan sanda
  • Dan'uwanta yayi fatan ta zama Sifeto Janar wata rana

Hotunan wata kyakkyawar jami'ar yan sandan Najeriya sun bayyana a kafafen ra'ayi da sada zumunta kuma mutane na tofa albarkatun bakinsu.

Jami'ar mai suna Fatima AbdulAziz 'yar asalin karamar hukumar Malumfashi a jihar Katsina ce kuma tana da girman Mataimakiyar Sufritandan DSP.

A hotunan da aka daura a shafin Officers and Cadets na Facebook, an ga jami'ar cikin kayan yan sanda mai ban sha'awa.

Hotunan jami'ar yan sanda 'yar Katsina da ake ganin itace mafi kyau a Hukumar
Hotunan jami'ar yan sanda 'yar Katsina da ake ganin itace mafi kyau a Hukumar Photo Credit: Officers and Cadets worldwide
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Bayan kwanaki 6 hannunsu, yan bindiga sun saki yayan sakataren jihar Katsina

'Dan uwanta na addu'an ta zama IGP nan gaba

Dan'uwanta mai suna Abdulaziz Bin Abdulaziz, yayi addu'an yar uwarsa ta zama shugabar yan sandan Najeriya wata rana.

Legit ta lalubo wannan addu'a da yayi kimanin shekaru hudu da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel