Jami'ar Bayero ta karawa Dr. Sani Rijiyan Lemo matsayi zuwa mataimakin Farfesa

Jami'ar Bayero ta karawa Dr. Sani Rijiyan Lemo matsayi zuwa mataimakin Farfesa

  • Yan kwanaki bayan samun sabon matsayi, Dr Sani Umar Rijiyar Lemo ya zama Farfesa
  • Dakta Sani na cikin jerin manyan Malaman da jami'ar ta yiwa karin girma
  • Mutane da dama sun taya Malamin murna da san barka

Kano - Jami'ar Bayero dake jihar Kano ta karawa shahrarren Malaman addinin Musulunci, Dakta Sani Umar Rijiyar Lemo matsayi zuwa na mataimakin Farfesa, rahoton Aminiya.

A cewar rahoton, Dr Sani wani Malami ne a tsangayar Adabi da Ilimin Addinin Musulunci a jami'ar ya samu karin matsayi ne bisa gudunmawarsa a bangaren ilimi da bincike.

Wannan na zuwa ne yan kwanaki bayan nada shi shugaban cibiyar nazarin addinin Musulunci da muhawarar addinai a jami'ar BUK.

Bayan Dr Umar Sani, akwai wasu Malamai da jami'ar ta karawa matsayi daga manyan Lakcarori zuwa mataimakan Farfesoshi.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa ya yi sabon nadi, ya ba Osinbajo sabon aiki, ya nada shugaba a hukumar NCDC

Hakazalika wadanda aka karawa matsayi zuwa cikakkun Farfesoshi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami'ar Bayero ta karawa Dr. Sani Rijiyan Lemo matsayi zuwa mataimakin Farfesa
Jami'ar Bayero ta karawa Dr. Sani Rijiyan Lemo matsayi zuwa mataimakin Farfesa Hoto: Dr. Muhd Sani Umar R/lemo
Asali: Facebook

Daga cikin sauran Malaman da aka karawa matsayi zuwa mataimakin Farfesoshi sun hada da:

1. Umar Sani Fagge – Sashen Larabci

2. Aliyu Harun – Sashem Ilimin Addinin Musulunci

3. Nura Sani – Ilimin Addinin Musulunci

4. Ahmad Salisu – Larabci

5. Matabuli Shehu Kabara - Larabci

Daga cikin wadanda aka yi wa karin girma zuwa farfesa su ne:

1. Shehu Ahmad – Harshen Larabci

2. Usman Sani Abbas – Ilimin Addinin Musulunci

3. Sani Ayagi – Ilimin Addinin Musulunci

4. Umar Abdulkadir – Ilimin Addinin Musulunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng