Shekaru 6 kenan Ganduje ya ki biyana kudin fansho, Kwankwaso

Shekaru 6 kenan Ganduje ya ki biyana kudin fansho, Kwankwaso

  • Kwankwaso ya yi korafin yadda gwamna Ganduje ke take masa hakkinsa
  • Tsohon gwamnan yace ba'a biyansa kudin fanshon wata-wata da ya kamata
  • Kwankwaso ya hadu da Ganduje a filin jirgin sama a Abuja makon da ya gabata

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano karkashin Gwamna Abdullahi Ganduje na take masa hakkinsa.

Kwankwaso ya yi korafin cewa shekara shida kenan Ganduje ya ki biyansa kudin fansho, ya ki gina masa gida kamar dokar jihar ta tanada.

Hakazalika gwamna Ganduje bai gina masa ofishin da doka ta bukaceshi ba.

Kwankwaso ya ce an yi hakan ne da gangan saboda ya koma jam'iyyar hamayya.

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da BBC Hausa.

Kara karanta wannan

Allah ne ya haɗa mu: Kwankwaso ya magantu kan haɗuwar shi da Ganduje

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Da ace ina tare da su, da sun biya ni kudaden fansho na a kowanne wata. Na yarda hakan na faruwa ne saboda ina bangaren adawa. Saboda haka su je su rike."

Shekaru 6 kenan Ganduje ya ki biyana kudin fansho, Kwankwaso
Shekaru 6 kenan Ganduje ya ki biyana kudin fansho, Kwankwaso Hoto: AIT
Asali: Facebook

Allah ne ya haɗa mu: Kwankwaso ya magantu kan haɗuwar shi da Ganduje

A wani sashen hirar, Rabiu Musa Kwankwaso ya bada labarin yadda suka hadu da wanda ya gaje shi, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja

Kwankwaso ya ce ya kwashe kusan sa'a 1 a wurin jira bayan an sanar da shi cewa Ganduje yana kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin.

Yace:

"Na ce ba komai, Allah ne ya hada mu. Wurin kamar tasha ce, babu wanda zai ce wa wani ya zo ko kada ya zo. Ya zo, mun gaisa da juna."

Kara karanta wannan

Rigingimu 10 da suka jawo Sabo Nanono da Saleh Mamman suka rasa kujerun Ministoci

Rikicin cikin gida zai iya tarwatsa mu, Kwankwaso ya ja kunnen shugabannin PDP

Kwankwaso ya ce rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar PDP ya na iya tarwatsa jam'iyyar baki daya.

Kwankwaso ya ce ba a bukatar irin wannan rikicin a wannan lokacin da jam'iyyar ke fama da rasa mambobin ta.

Yace:

"A yanzu karfin jam'iyyar ya ragu kuma a karshe abinda zai faru shi ne za mu tarwatse baki daya."
"Ka ga wannan sakamakon ba zai taimake mu ba saboda ba mu da shugaban kasa kuma ba mu da gwamnoni masu yawa,"

Asali: Legit.ng

Online view pixel