Jiga-jigan APC sun ajiye bambance-bambancen cikin-gida domin a doke PDP a zaben Kaduna

Jiga-jigan APC sun ajiye bambance-bambancen cikin-gida domin a doke PDP a zaben Kaduna

  • Sanata Uba Sani ya yi kira ga ‘Ya ‘yan jam’iyyar APC su hada-kansu a Kaduna
  • Shugaban Majalisa, Yusuf Zailani ya bi sahu, ya nemi ‘Yan APC su yafe wa juna
  • ‘Yan siyasar sun hada-kansu yayin da ake shiryawa zaben kananan hukumoni

Kaduna - Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisa, Uba Sani, ya yi kira ga fusatattun ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki su ajiye kayan fadansu.

Jaridar Premium Times tace Sanata Uba Sani ya yi wannan kira ne yayin da ake shirin gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi a Kaduna.

Uba Sani ya halarci taron masu ruwa da tsaki na zaben da za a gudanar a ranar Asabar, 4 ga watan Satumba, 2021, ya yi kira ayi hakuri, a yafe wa juna.

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisar PDP sun zargi Jami’an tsaro da hada-kai da ‘Yan bindiga a jihar Arewa

Abin da Uba Sani ya fada a taron

“Mu yafe wa juna, mu hada-kai, muyi aiki tare. Dole a dage domin ganin an lashe duka wasu kujeru a kananan hukumomi.”
“Nauyi ne a kan kowane daga cikinmu, ya yi kokari domin mu kai ga ci wa manufa guda.”

Rahoton yace shi ma shugaban majalisar dokoki na Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Zailani, ya jaddada irin wannan kira, yace akwai bukatar ‘yan APC su hada-kai.

Nasir El-Rufai
Gwamna Nasir El-Rufai ya na kamfe Hoto: www.sunnewsonline.com
Asali: UGC

Sai da hakuri - Zailani

Rt. Hon. Yusuf Zailani ya yi kira ga ‘ya ‘yan jam’iyyar APC su guji zargin juna da nuna wa juna yatsa, yace ta haka ne kurum za a iya kai ga nasara a zaben.

“Mu yi hakuri, duk ‘Dan Adam yana kuskure; Ubangiji ne yake bada mulki ga duk wanda Ya so.”

Kara karanta wannan

Na ƙosa in ga ka yi nasara, Buhari ya faɗa wa ɗan takarar gwamnan APC a Anambra, Andy Uba

Yusuf Zailani wanda ake yi wa kallon abokin gaban Sanata Uba Sani, ya yi kira ga shugabannin APC su zama abin koyi, su tafi da duk wani ‘dan jam’iyyar APC.

Za ayi amfani da na'urorin zamani a zaben Kaduna

A halin yanzu ana horas da ma’aikatan da za su yi aikin wannan zabe da za ayi a ranar Asabar.

Hukumar gudanar da zabe ta jihar Kaduna za ta sake yin zaben da na’urorin zamani, abin da ba a taba gani an yi a wata daga cikin jihohin da ke Najeriya ba.

Seconudus ya ga ta kansa

A lokacin da a ake nema ayi sulhu, sai aka ji an dakatar da Prince Uche Secondus bayan kotu ta tsige shi daga kujerar shugaban jam'iyyar adawa ta PDP.

Shugabannin PDP na karamar hukumar Andoni a jihar Ribas, sun yi waje da shugaban na su, suka ce babu wani abin da Uche Secondus ya tsinana masu.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi luguden wuta, sun kashe ‘Yan bindiga rututu da su ka fake a jejin Zamfara

Asali: Legit.ng

Online view pixel