Rashin tsaro: A fito a fadi gaskiya, Shugaba Buhari ya ci amanarmu inji ‘Dan Majalisar Katsina

Rashin tsaro: A fito a fadi gaskiya, Shugaba Buhari ya ci amanarmu inji ‘Dan Majalisar Katsina

  • Hon. Aminu Garba Danmusa ya caccaki gwamnatin Muhammadu Buhari
  • ‘Dan majalisar yace an gagara a shawo kan matsalar tsaro a jihar Katsina
  • Hon. Danmusa yace tulin kuri’un da Katsina ta ba Buhari bai yi amfani ba

Katsina - ‘Dan majalisa mai wakiltar mazabar Danmusa a mazabar jiha, Aminu Garba Danmusa, yace shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ci amana.

Jaridar Katsina Post ce ta rahoto Honarabul Aminu Garba Danmusa yana cewa Mai girma shugaba Muhammadu Buhari ya ci amanar mutanen Katsina.

Aminu Garba Danmusa ya bayyana wannan yayin da yake koka wa kan yadda ake fama da matsalar tsaro a mazabarsa da wasu bangarorin jihar Katsina.

Rahoton ya tattaro abin da ‘dan majalisar ya fada, inda ta ce an tafa masa a lokacin da yake cewa shugaba Muhammadu Buhari ya ci amanar Katsinawansa.

Kara karanta wannan

Tsohon ministan Afghanistan ya koma sana'ar siyar da abinci a kasar Jamus

Me Hon. Danmusa ya fada?

“Ba yau na fara ba, zan yi magana a kan shugaban kasa. An yaudari mutanen Katsina, mun ba shi kuri’ar da ta fi yawa a Najeriya, domin zama shugaban kasa.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Kamar yadda abokan aiki na suka koka, a jiya sun shigo garin Danmusa, suka auka wa wani kauye da ake kira Marken dambi, suka kashe wani Bawan Allah.”

Buhari decorates new Army chief
Buhari da sabon hafsun sojan kasa Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Bayan ‘yan bindiga sun hallaka wannan mutumi, ‘dan majalisar yace an dauka matarsa da diyarsa.

'Dan majalisa ya yi kira ga shugabanni

“Maganar gaskiya abin ya fi karfinmu. Allah madaukakin Sarki da Buhari kadai za su iya magance kalubalen nan. Zai iya yin wannan a cikin kwana bakwai.”
“Laifin me muka yi a Katsina, mun zabe shi ya zama shugaban kasarmu, amma yau Katsina ta fi kowace jiha shan wahalar rayuwa da rashin zaman lafiya.”

Kara karanta wannan

Obasanjo: Masu son ganin rabewar kasar nan makiyanta ne, za su ji kunya

“Na rantse da Allah gara mu daina boye-boye, mu fada wa kanmu gaskiya, wannan ba zai fishe mu ba."
“Mu da aka zaba, muna yaudarar kanmu, mu tattara mu je mu samu mutumin nan, mu tambaye shi wani zunubi muka yi ba zai iya maganin miyagun nan ba.”

'Yan majalisar Katsina sun zubar da hawaye

A makon da ya gabata ne aka dauko batun yadda tsaro ya tabarbare a zauren majalisar dokokin Katsina. Har ta kai wasu 'yan majalisar sun yi kuka da idonsu.

‘Dan majalisar yace ana dauke mutane, ayi wa yara fyade gaban iyayensu, amma ba za a iya komai ba.

An ji Hon. Dalhatu-Tafoki mai wakiltar Faskari yana cewa duk da kokarin gwamnatin tarayya da na jihohi, da hukumomin tsaro, har gobe a kan kai hare-hare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel