Mutum milyan biyu ke ta'amuni da kwaya a jihar Kano, Janar Buba Marwa

Mutum milyan biyu ke ta'amuni da kwaya a jihar Kano, Janar Buba Marwa

  • Hukumar NDLEA ta kama mutane 8000 masu shan kwaya a jihar Kano a shekarar nan kadai
  • Kimanin mutum milyan biyu ke ta'amuni da kwayoyi a jihar, cewar shugaban NDLEA

Kano - Shugaban Hukumar dakile ta'amuni da muggan kwayoyi a Najeriya, NDLEA, Buba Marwa, ya bayyana cewa mutum milyan biyu ke ta'amuni da kwaya a jihar Kano kadai.

Marwa ya bayyana hakan ne yayinda ya kaiwa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ziyara ranar Litnin.

A cewarsa:

"A jihar Kano, kashi 16 cikin 100 na ta'amuni da kwaya; hakan na nufin cewa cikin kowani mutum shida, mutum daya dan kwaya ne kuma masu shekaru tsakanin 15 da 64."
"Jihar Kano na da kimanin mutum milyan biyu masu amfani da Tramol, Kodin, da wasu magungunan tari, sabanin wiwi."

Kara karanta wannan

Musulunci Ya Haramta: Ban Goyon Bayan Halasta Amfani Da Wiwi, Ƴan Majalisar Kano Ma Basu Goyon Baya, Ganduje

Mutum milyan biyu ke ta'amuni da kwaya a jihar Kano, Janar Bubar Marwa
Mutum milyan biyu ke ta'amuni da kwaya a jihar Kano, Janar Bubar Marwa HotoL NDLEA
Asali: Facebook

An kama mutane 8000 masu amfani da kwaya a Kano

Janar Marwa yace daga watan Junairu zuwa yanzu, hukumar karkashinsa ta kama mutum dubu takwas kuma da dama cikinsu na gidajen yari yanzu haka.

"Tun da na zama shugaban NDLEA a Junairu, mun kwace kilo milyan biyu na kwayoyi, na biliyoyin Naira."
"An damke mutum dubu takwas kuma 1,699 na cikin kurkuku yanzu, kuma har yanzu muna aiki."
"Ta'amuni da muggan kwayoyi ya fara tarwatsa iyalai da dama muddin ba'a dau mataki ba."

Marwa yace amfani da wadannan kwayoyi sun kara yawan laifuka irinsu barandanci, garkuwa da mutane, fashi da makami, dss.

Ya yi kira ga gwamnatin jihar ta kafa dokar wajabta gwajin kwaya ga dukkan wadanda ke shirin aure.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Zan yi maganin masu ta da hankali da kashe-kashe a Jos

Asali: Legit.ng

Online view pixel