Kashe-kashen Jos: Gwamnatin jihar Kaduna ta kwashe dalibanta daga jami'ar UniJos

Kashe-kashen Jos: Gwamnatin jihar Kaduna ta kwashe dalibanta daga jami'ar UniJos

  • Gwamnatin jihar Kaduna ta kwashe dalibai yar asalin jihar dake karatu a jami'ar Jos
  • Shugaban ma'aikatar bada tallafin karatu na jihar, Hassan Rilwan, ya bayyana adadin daliban da suka kwashe kawo yanzu
  • Rikici da kashe-kashe sun wajabtawa gwamnatin jihar Plateau kulle makarantar

Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta fara kwashe dalibai yan asalin jiharta dake karatu digirinsu daga jami'ar Jos, da sauran makarantun gaba da sakandare dake jihar Plateau.

Jaridar Punch ta bayyana cewa Sakataren hukumar bada da tallafin karatu da bada basussuka na jihar Kaduna, Hassan Rilwan, ya fadi hakan.

Rilwan yace a ranar Juma'a 20 ga watan Agusta, jami'an tsaro sun kwashe dalibai 87.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar za ta cigaba da kokarinta wajen kare rayukan daliban jihar Kaduna dake jihar Plateau.

Kara karanta wannan

Rikicin Jos: Jihar Kaduna ta kwashe dalibai 'yan jiharta dake karatu a jihar Filato

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kashe-kashen Jos: Gwamnan jihar Kaduna ta kwashe dalibanta daga jami'ar UniJos
Kashe-kashen Jos: Gwamnan jihar Kaduna ta kwashe dalibanta daga jami'ar UniJos Hoto: UJ
Asali: UGC

An kashe dalibin jami’ar Jos ‘yan awanni bayan Lalong ya saukaka dokar kulle

Rahotanni sun kawo cewa wasu ‘yan daba sun caka wa wani dalibin jami’ar Jos wuka har lahira a kusa da makarantar.

Lamarin ya faru ne ‘yan awanni bayan da gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong ya sassauta dokar hana fita ta sa’o’i 24 a karamar hukumar Jos ta Arewa.

An tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 2:30 na rana lokacin da harkoki ke komawa daidai a hankali a babban birnin jihar.

Shuaban kungiyar dalibai ta jami’ar (SUG), Kwamared Danladi Joshua Adankala, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Jos.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng